An Cafke Mutumin Da Ya Kashe Tsohuwa Ya Sayar Da Sassan Jikinta

Ana zargin wani mutum mai suna Dauda Bello, mai kimanin shekara 54 da laifin kashe wata tsohuwa mai suna Misis Mesesi Adisa da sayar da sassan jikinta.

Majiyarmu ta shaida mana cewa, bayan kama wanda ake zargin, ranar 7 ga watan Yuli, ya tabbatar wa da yansanda, yadda ya kashe wannan tsohuwa, ya kuma sayar da kafadunta da kuma kafafunta.

Marigayiyar Misis Adisa ta bata bat ne jim kadan bayan fitowarta daga gidan ta.

Bayan faruwar wannan lamari ‘yan’uwan marigayiyar sun kai rahoto ofishin yansanda na Sabo-Ilupeju, daga baya kuma suka koma ofishin masu yaki da masu garkuwa da ke sashin binciken manyan laifuka.

Labari Mai Alaqa>>> Mahaifina Yana Biyana Naira 30,000 In Sato Masa Yara – Wata Budurwa Hausatiktok.com.ng

SP Taiwo wanda ke gudanar da bincike kan wannan lamari, yace; “guri na karshe da marigayiyar tsohuwa ta je shi ne, gidan wanda ake zargi da ke yankin Olodo a Abeokuta ta Arewa cikin jihar Ogun”.

“Mai Magana da yawun rundunar yansanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, yace; an tsare wanda ake zargin a ofishin yansanda, domin ci gaba da gudanar da bincike”.

Binciken da muka fara, wanda ake zargin ya tabbatar da cewa, sun dade suna sayar da mutane shida tsohuwa.

Ya kara da cewa shi ne ya kira marigayiyar zuwa gidansa, domin su tattauna kan kasuwancinsu na sayar da mutane, sai lokacin da suke gana wa a gidansa, ya fahimci cewa, tsohuwa tazo da wasu kudi masu yawa.

Yadda Ya Kashe Tsohuwa

Wannan yasa, yakai mata duka a kanta da wani katon katako, wanda kuma nan take ta fadi kasa sumammiya, ganin cewa ta mutu, sai ya dauki gawar tsohuwa ya kai ta daji ya jefar.

See also  Yadda Wani Tsoho Ya Auri Jikarsa Yaki Kuma Yarda Ya Sake Ta A Jihar Zamfara - Hausatiktok.com.ng
Tsohuwa
Dauda Bello, mai kimanin shekara 54 da laifin kashe wata tsohuwa

Oyeyemi yace; wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin, bayan kashe matar ya kuma lalube ta, wanda ya samu naira 22,200 a wajenta, bayan wannan danyen aiki sai ya gudu.

Da yayi tunanin zai samu kudi masu yawa a wajen wannan tsohuwa, amma sai ya ga babu kudin da yake tsammani a gareta.

A karshe, wanda aka kaman ya kai yansanda dajin da ya binne gawar wannan tsohuwar mata, sannan kuma ya nuna wa yansanda wasu sassan jikin tsohuwa matar da ya cire a jikinta.

Kwamishinan yansanda, Lanre Bankole, ya bada umarni a gaggauta gurfanar da wanda ake zargin gaban kuliya, domin yi masa hukunci da yakamata Kan kisan tsohuwa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *