Yadda Wani Tsoho Ya Auri Jikarsa Yaki Kuma Yarda Ya Sake Ta A Jihar Zamfara – Hausatiktok.com.ng
Wani tsoho, Alhaji Musa Tsafe dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamafara, ya ki amince wa ya saki wata Jikarsa da ya aura tsawon shekaru 20. TSOHO – hausatiktok.com.ng
Alhaji Musa ya yanke shawarar kin sakin jikar tasa ce mai suna Wasila Isah Tsafe yar shekara 35 bayan an sanar da shi cewa auren na su haramtacce ne.
Matar tasa, Wasila Tsafe, ta haifar wa Alhaji Musa yara 8.
An rahoto cewa, “an sanar da Masarautar Tsafe kan maganar auren, inda dattawan afadar suka yiwa Alhaji Musa kiranye,
bayan gudanar da bincike aka sheda wa Alhaji Musa cewa, auren na sa da jikarsa bisa sharudan addinin musulunci haramtacce ne”.
Hakazalika, “Malaman addinin musulunci sun shawarci Musa ya saki Jikarsa da yake aure,
Wasila Tsafe amma lamarin ya cutura ga Alhaji Musa Inda yace hakan ba za ta sabu ba”.

Biyo bayan tirjiyar da Alhaji Musa ya yi, Hukumar Hisba ta karamar hukumar Tsafe ta maka Alhaji Musa kara a gaban Babbar kotun shari’ar Musulunci dake Jihar Zamfara.
kotun ta sa ranar da 21 ga watan Yulin 2022 ranar sauraron karar.
Labari Mai Ban Sha’awa>>Ya’yan Buhari Biyar Da Ya Aurar Bayan Zama Shugaban Kasa
Labari Na Gaba>>> Buhari Ya Taya Sanata Ademola Na Jam’iyyar PDP Murnar Lashe Zaben Gwamnan Osun
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya dan takarar kujerar Gwamna a Jam’iyyar PDP murnar lashe zaben Gwamnan jihar Osun
da aka gabatar a ranar Asabar, an Bayyana sakamako a ranar Lahadi, 17 Ga Watan Yuli, 2022.
Buhari ya Bayyana haka ne a shafinsa na Kafar sada zumunta na manhajar Facebook a safiyar Ranar Lahadi.

“Ina taya Sanata Ademola Adeleke, dan takarar jam’iyyar PDP murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan Osun.
Al’ummar jihar Osun sun zabi ra’ayinsu ta hanyar jefa kuri’unsu”.
Wannan itace ma’anar dimokuradiyya, mutunta ra’ayin jama’a.
“Nasarar gudanar da shirin zaben Jihar Osun ya nuna isar cikar Kamala da jajircewar duk masu ruwa da tsaki,
wajen karfafa sahihancin tsarin zabe a Najeriya”.
Har kullun, “zan cigaba da jajircewa matuka wajen tabbatar da barin gadon Gaskiya da gudanar da sahihin zabe a Najeriya.” Shugaban Kasa Mummadu Buhari”.