Ba Zamu Iya Ciwo Bashin N1.1trn Ba Saboda Yajin Aikin ASUU – Festus Keyamo

Ba Zamu Iya Ciwo Bashin N1.1trn Ba Saboda Yajin Aikin ASUU – Festus Keyamo

Karamin Ministan Kwadago, Mr. Festus Keyamo, ya bayyana cewa; Gwamnatin Tarayya ba za ta iya ciwo bashin Tiriliyan N1.1trn a duk shekara don warware matsalar ASUU ba.

Ministan Kwadagon ya nemi kungiyar ASUU su janye yajin aiki saboda basu kadai bane hukumar dake ci daga Asusun gwamnatin Tarayyar Najeriya ba.

Mr. Festus Keyamu ya bukaci iyayen dalibai a fadin kasar su roki kungiyar ASUU su janye Sannan su bar malamai su koma bakin aikin su.

Festus Keyamo, Karamin Ministan Kwadago, ya bayyana a jiya cewa.

Gwamnatin Tarayya ba ta da hurumin ciyo bashin Naira Tiriliyan 1.2 a duk shekara domin warware yajin aikin da kungiyar Malaman Jami’o’i wato (ASUU) suka shiga.

Karanta Wannan: University of Toronto: Lester Pearson Scholarships for International Students 2022

RAHOTO

Rahotanni daga THE NATION Martanin Festus Keyamo kenan a lokacin da yake amsa tambayoyi a gidan talabijin na Channels TV.

Keyamo yace; “matsin lamba kungiyar ASUU ba zata sa gwamnati ta ciyo bashin Naira Tiriliyan 1.2 dan biyan bukatun ta ba”.

Wanda idan aka yi la’akari adadin kudin shiga da kasar take samu, bai wuce Naira Tiriliyan 6.1, a lokacin da muke da hanyoyi, da kuma cibiyoyin kiwon lafiya da zamu gina, ga kuma sauran fannoni da ke bukatar kulawa a kasar.

Duba Wannan: Taibah University Scholarships for International Students 2022

Daga nan sai Mr. Festus Keyamo ya bukaci iyaye a fadin kasar da su rika rokon kungiyar ASUU ta janye yajin aikin da tajima ta keyi.

Keyamo ya kara cewa; “yakamata su koma bakin aikin su, saboda basu kadai bane hukumar dake ci daga asusun Najeriya ba, Najeriya baza ta tsaya cak saboda an kasa biyan bukatun ASUU ba”.

See also  Matsalar Tsaro: Osinbajo Ya Bukaci Sojoji Da Suyi Bayanin Kudaden Da Suka Basu

Saboda haka kusan abunyi ku kuma gaggauta janye Yajin aikin ku cigaba da shiga aji.

Karin Labari: Bazan Barwa ‘Ya’yana Gado Ba – Shugaba Buhari

(Ba Zamu Iya Ciwo Bashin)

Ku Cigaba Da Bibiyar Wannan Shafi Domin Samun Sahihan Labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *