Har Yanzu Ni Masoyin Buhari Ne, inji Fasinjan Da Ya Kubuta Daga Hannun Yan Ta’adda
Har Yanzu Ni Masoyin Buhari Ne, inji Fasinjan Da Ya Kubuta Daga Hannun Yan Ta’adda.
Hassan Usman, lauya ne kuma daya daga cikin wa’inda harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su, ya fada cewa shi har yanzu masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.
A ranar 28 ga watan Maris daya gabata, wasu yan bindiga sun kai hari kan wani jirgin kasa dauke da dubban Mutane, da ke kan hanyar Kaduna.
Inda aka kashe mutane da dama, aka kashe wasu, wasu sun jikkata, kuma anyi awon gaba da wasu.
Karanta Wannan: Ba Zamu Iya Ciwo Bashin N1.1trn Ba Saboda Yajin Aikin ASUU – Festus Keyamo
Hassan na daga cikin fasinjoji hudu da aka sako daga hannun masu garkuwar da mutane a ranar 25 ga watan Yuli daya gabata.
Da yake magana a wata hira da ICIR sukayi dashi, yace “duk da cewa gwamnati mai ci ta gaza a fannin tsaro, amma har yanzu “Ni ina matukar kaunar Muḥammadu Buhari”.
Har yanzu ni masoyin Buhari ne, amma ta fuskar tsaro zan iya baiwa wannan gwamnati maki kadan.
Domin daya daga cikin babban nauyin da ke wuyansu shi ne ganin gwamnati ta tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar nan, inji shi.
Hassan Usman
Labarai: Sunusi Lamido – Najeriya Ta Tabar-bare Fiye Da Yadda Take A 2015
Amma kamar yadda yake a yanzu, zan iya cewa gwamnati ta gaza sosai a fannin tsaro.
Duk da dumbin makudan kudaden da ake ware wa domin tsaro a Najeriya, babu wani abu da ake gani a kasa, kwalliya bai biya kudin sabulu ba.
Ya kara da cewa abin da ya fuskanta a lokacin da yake tsare yana da matukar muni kwarai da gaske, abun badadi.
Wannan abunda ya fada yayi ta yawo a kafafen sada zumun ta, da gidajen Labarai, anji ra’ayoyin mutane da dama akai wanda mafi akasarin su sunce yasamu tabin hankali.
Duba Wannan: Matsalar Tsaro: Osinbajo Ya Bukaci Sojoji Da Suyi Bayanin Kudaden Da Suka Basu
Ku Cigaba Da Bibiyar Wannan Shafi Domin Samun Sahihan Labarai.