Isra’ila Tayi Wa Falasdinawa Luguden Wuta A Gaza
Isra’ila Tayi Wa Falasdinawa Luguden Wuta A Gaza
Shugaban kungiyar mayakan Falasdinawa ta Islamic Jihad ya sha alwashin kai hari a birnin Tel Aviv,
bayan wani mummunan harin da Isra’ila ta kai ta tare da kashe daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar a zirin Gaza, yayin da mutane 44 suka jikkata a yayin harin.
Izuwa yanzu dai adadin wadanda suka mutu a sakamakon harin bayan babban jagoran na mayakan Falasdinawan,
Da kuma mutane 15, yayin da gidajen mutane da dama suka ruguje Lokacin da aka kai hare haren.
An hango yadda bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya bayan harin, abin da ya tunzura hukumomin Gazan da ke ganin hakan tamkar wata takalar fada.
Karanta Wannan: China ta Yanke dangantaka da Amurka
A cewar kungiyar tuni aka yi jana’izar babban kwamandan, Mai suna Tayseer Al-Jabari Abu-Mahmud, wanda ya mutu da safiyar ranar Juma’a ta cikin sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar.
Dakarun Gaza da wasu kananan yara hudu na cikin wadanda suka rasa rayukansu tare da jagoran a harin da Isra’ilan ta kai wa falasdinawa.
Labarai Masu Alaka: Matsalar Tsaro: Osinbajo Ya Bukaci Sojoji Da Suyi Bayanin Kudaden Da Suka Basu
Tuni dai kakakin rundunar sojin Isra’ila yace; “yanzu Gaza ta fara ganin irin wadannan hare-hare, don kuwa ba za ta gaza ba har sai ta kakkabe mayakan baki daya daga yankin”.
(Isra’ila Tayi Wa Falasdinawa)
Ku Cigaba Da Bibiyar Wannan Shafi Domin Samun Sahihan Labarai.