Matsalar Tsaro: Osinbajo Ya Bukaci Sojoji Da Suyi Bayanin Kudaden Da Suka Basu

Matsalar Tsaro: Osinbajo Ya Bukaci Sojoji Da Suyi Bayanin Kudaden Da Suka Basu

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Prof. Yemi Osinbajo ya bukaci sojojin kasar nan da suyi wa al’umma bayani kan irin ma’kudan kudaden da gwamnati take basu domin gudanar da ayyukan tsaro a karkashin Shugabancin Muhammadu Buhari tun daga hawan su kan kujera.

Osinbajo ya ce: “Al’ummar kasa na da hurumin sanin irin makudan kudaden da wannan gwamnati ta ware domin tinkarar matsalolin tsaron da suka addabi Kasar Najeriya, wanda ke kaiwa ga rasa dubban rayuka, dan kore shakku dangane da yadda gwamnati ke fuskantar kalubalen da tabar-barewar tsaro”.

Labarai Masu Alaka: Zamu Sace BUHARI Da El-Rufai A Wani Sabon Bidiyo – Yan Bindiga

Mataimakin shugaban kasar ya sake
cewa: “Abin takaici ne kowanne lokaci idan anyi maganar tsaro, sai kaji wasu sojojin na cewa basu da kayan aiki”.

Saboda haka ya dace ma’aikatar tsaro ta gabatar da wani tsari wanda zai dinga bayyana irin kudaden da suke kashewa wurin hidiman tsaron a kasar.

Osinbajo ya bayyana cewar ya dace ace Najeriya ta shawo kan matsalar yan bindigar da ake fama da ita, ta wajen nuna kwarewa da kuma nuna dabarun yaki kala-kala.

Wata Majiya wato Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya, ta gabatar da kasafin kudin tsaron da aka baiwa ma’aikatar tsaro tun shigowar gwamnatin Muḥammadu Buhari a shekarar 2015 kamar haka:

Duba Wannan: Boko Haram: Zulum visits Chad to honor 6,000 multinational forces

Makudan Kudaden Da Ake Bama Jami’an Tsaro a Najeriya

1. 2015 – Naira biliyan 968

2. 2016 – Naira Tiriliyan guda da miliyan 700

See also  Yan Sanda Sun Samu Nasarar Kama Manyan Barayi Da Suka Addabi Birnin Katsina Tareda Karbo Motoci 13 Daga Hannun Su

3. 2017 – Naira Tiriliyan guda da miliyan dubu 1 da 500

4. 2018 – Naira Tiriliyan guda da miliyan dubu 1 da 350

5. 2019 – Naira Tiriliyan guda da miliyan dubu 1 da 400

6. 2020 – Naira Tiriliyan guda da miliyan dubu 800

7. 2021- Naira Tiriliyan guda da miliyan dubu 960 da kuma kasafi na musamman Naira biliyan 722 da miliyan 530.

Kamar yadda kuka gani wannan shine kasafin kudin da ake warewa don Tsaro a kassr mu ta Najeriya.

(Matsalar Tsaro: Osinbajo Ya)

Ko Mai Zaku Iya Cewa? Ku Aiko Mana Da Ra’ayoyin ku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *