Wata Mata Ta Maka Mijinta A kotu Saboda Ya Buya A Bandaki Lokacin Da Yan Fashi Suka Shiga Gidansu
Wata Mata Ta Maka Mijinta A kotu Saboda Ya Buya A Bandaki Lokacin Da Yan Fashi Suka Shiga Gidansu.
Wata mata mai suna Asiajo Oladejo ta kai karan mijinta a kotu bisa buya a bandaki lokacin da yan fashi su ka shiga gidansu.
Mrs. Oladejo, ta yi karar mijin nata mai suna Abidemi a gaban kotun majistire da ke Mafo a garin Ibadan, Jihar Oyo Najeriya.
Labari: Har Yanzu Ni Masoyin Buhari Ne, inji Fasinjan Da Ya Kubuta Daga Hannun Yan Ta’adda
Ta shaida wa kotun cewa mijin nata ba abokin zama ba ne tun da ya kasa kare ta lokacin da bala’i ya afko musu, inda take cewa sai dai ma yayi ta kansa ba ta iyalinsa ba.
Hakan yanuna cewa baisamu da mu ko kadan, kanshi kawai yasani.
Ta kara da cewa, ta shiga halin firigici a lokacin da yan fashin su ka shigo gidan nasu,
inda ta nemi mijin nata domin ya kawo musu dauki ya taimaka kesu ita da ya’yan ta (iyalansa), amma ta neme shi ta rasa, a she yana cikin bandaki ya kulle kansa.
Karanta Wannan: Ba Zamu Iya Ciwo Bashin N1.1trn Ba Saboda Yajin Aikin ASUU – Festus Keyamo
Ta ce yan fashin sun yi abinda suka ga dama a gidan, inda bayan sun tafi ne sai ga mijin nata Abidemi ya fito daga bandaki, sabo da haka take nema kotu ta raba auren nasu.
Kotu
Ko da alkali ya wai-wayi wanda a ke karar, sai ya amsa cewa tabbas ya buya a bandaki, amma ya bata hakuri, kuma ba yadda bai yi da ita ba akan ta dawo gidansa su cigaba da zama tare amma ta’ki yarda.
Ya kuma roki kotu da ta bar masa ya’yan su guda uku a hannunsa, inda yace kowa ya san cewa shi yana kuka da ya’yan sa.
Da take yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a SM Akintayo, ta ki karbar korafin mijin nata, inda ta ce matar zata fi kulawa da su fiye dashi, amma su biyun ne za su dauki nauyin karatun yaran, ta kuma raba auren nasu nan take.
Yanzu dai bashi ba ita saidai Ya’yan da suke dashi, aure an riga an raba a kotu.
Duba Wannan: Sunusi Lamido – Najeriya Ta Tabar-bare Fiye Da Yadda Take A 2015
(Wata Mata Ta Maka)
Ku Cigaba Da Bibiyar Wannan Shafi Domin Samun Sahihan Labarai.