YADDA ZA KA SAYI DATA MAI SAUKI DA LAYINKA NA MTN

Assalam alaikum. Barkanku da wannan lokaci, muna fatan kuna jin dadin ziyartar wannan website din namu mai suna Hausatiktok. Com.Ng

A yau mun zo muku da wata garabasa, wannan garabasa za ta ba ka damar siyan data mai araha da kanka ta hanyar danna wasu lambobi da layinka na MTN.

Karanta wannan: Yadda Za Ka Kaiwa Hukuma Npower Kokenka (Complain) Cikin Sauki Kuma Su Karba.

 

Kasancewar mutane suna ta korafe-korafen yadda kudadensu ke shekewa a wajen siyan data wannan kafa mai albarka ta ga ya dace ta kawo muku wannan hanyar domin taimakon al’umma.

Ita wannan data za ka iya shiga ko’ina da ita, wato za ka iya:

 • Facebook
 • WhatsApp
 • Kallo a YouTube
 • Shiga Website
 • Twitter
 • Instagram
 • Snapchat
  Ko’ina za ka iya shiga da ita, ba a kebanceta da wani platform da ban ba.

 

Karanta wannan: Ba Za Mu Iya Ciyo Bashin N 11Trn Ba Saboda Yajin Aikin Asuu -Festus Keyamo

 

HANYAR SIYAN DATAR

Da farko dai dole sai da layin MTN za ka iya siyan wannan data, za ka danna * 121 # a hade suke ba sifas, sai ka danna alamar kira za ka ga ya kawo ma wani zabi kamar haka:

 1. TopDeal4ME
 2. Data4ME
 3. Recharge4ME
 4. Combo4ME

Sai ka zabi ‘TopDeal4ME’ a nan ne za ka ga wannan rahusa ta data. Data 200mb a kan kudi 50 tana yin tsawon sati 2 kafin ta yi expire. Sannan akwai 1Gb data akan kudi 200 ita tana tsawo sati biyu. Haka kuma akwai 1.5Gb a kan kudi 300 ita ma tsawo sati biyu. Wani lokacin kuma kawai sai dai ka ga ‘Data4ME’ sai ka shi nan din ka zaba ka saya.

See also  Nabaraska zai fara ɗaukar wani Sabon Shiri mai suna MIJIN TSULELIYA. Mahaifiyar Rarara Ceh Tsoliya……

TANBIHI

Ita wannan data sai ta yi tsawon sati biyu take expire. Sannan kuma idan ka sayi karama kamar ta 50 din can za ka iya kararta a yau ma ya danganta da shige-shiganka musamman ma ace kallo Video za ka yi online. Idan ka ga layinka bai kawo ma wanna rahusar ba, to layinka ba ya cikin eligibility sai dai ka nemi wani MTN din ka gwada. Sannan datar tana da karfi sosai wallahi, domin ni ma da ita nake amfani.

Allah Ya ba da sa’a. Muna fatan za ka kasance mai ziyartar wannan website a kai a-kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *