FREE SCHOLARSHIP: KARATU KYAUTA GA MASU SHA’AWAR KARANTAR B.SC NURSING A JIHAR JIGAWA
Dama ta sama: Karatu Kyauta Ga Masu Sha’awar Karantar B.Sc Nursing.
Gwamnatin Jihar Jigawa, tare da hadin gwuiwar Al-Istikama University, Kano State, suke sanar da al’umma cewa, sun bada damar karatun digiri kyauta a bangaran malaman jinya wato B.Sc Nursing ga masu sha’awar karantan bangaran.
Za a fara gudanar da karatun ga daliban da suke sha’awar karantar wannan bangare na malaman jinya ( B.Sc Nursing ) a cikin wannan zango na karatu da muke ciki wato 2022/2023.
MASU AMFANA DA KARATUN
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanar da cewa, wannan dama ta kebanta ne ga daliban da suke sha’awar karantar B.Sc Nursing ‘yan asalin Jihar Jigawa ( Jigawa State Indigene ).
ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA MAI SHA’AWAR KARATUN.
- Damar wannan karatu ta kebanta ne ga dalibai ‘yan asalin Jihar Jigawa.
- Dole ne mai sha’awar karatun ya kasance ya kammala babbar makarantar sekandare.
- Sannan kumu dole ne ya kasance samu credit a Mathematics, English language, Biology, Chemistry, da kuma Physics.
- Kada makin JAMB na mai sha’awar karatun ya gaza 160.
- Sannan kuma dole ne ya zabi Al-Istikama University a zabi na farko da na biyu a JAMB ( 1st and 2nd choose).
- Dole ne mai sha’awar karatun ya kasance yana da Indijin na Jihar Jigawa.
- Dole ne mai sha’awar karatun ya kasance yana da lambar waya, da asusun tura sako na Email.
YADDA ZA KA YI APPLY
- Mai sha’awar wannan karatu zai yi rubutacciyar wasika ta neman damar karatu. A adireshin mai karba zai sa Ofishin Permanent Secretary, Jigawa State, Ministry Of Health.
- Kananan hotuna guda biyi.
- Indijin da sauran takardunsa duk zai yi tattaki ya kai su Ofishin Kwmishina na Jihar Jigawa, Ministry Of Health, dake New Secretariat Complex Dutse. Jihar Jigawa.
RANAR RUFEWA.
Za a fara karbar takardun a ranar 17th ga wata August, zuwa ranar 26th ga watan August, 2022.
Allah Ya bada sa’a.