PORTAL NA CIKE AIKIN DAN SANDA ( POLICE FORCE) YA GYARU, ZA KA IYA CIKEWA DA WAYARKA YANZU

Masha Allah: Portal Na Cike Aikin Dan Sanda ( Police Force) Ya Gyaru, Za Ka Iya Cikewa Da Wayarka Yanzu.

Assalam alaikum. Barkanka da kasancewa da wannan website manu mai suna HausaTikTok.Com.Ng

Tun bayan da Hukumar ‘Yan Sanda ta bude portal dinta domin daukar sabbin ‘yan sanda, ranar 15 ga wata August, portal din nasu yake ba da matsala, wato ba ya bada damar cikewa wannan aiki ga masu sha’awar cike aikin.

Amma a yanzu haka portal din ya dawo aiki haikan, wannan ta sa hukumar take kara sanar da al’umma cewa a yanzu haka mutum zai iya shi ya cike aikin na Dan Sanda cikin sauki.Y

ADDA ZA KA CIKE AIKIN DAN SANDA.

Idan ba ku manta ba a posting dinmu na baya mun yi cikekken bayani game da abubuwan da wannan hukuma take bukata ga masu sha’awar aikin na Dan Sanda. Duba abubuwan da suke bukatar a nan ” Abubuwan Da Hukamar ‘Yan Sanda Take Bukata Ga Mai Sha’awar Aikin

Bayan ka Shiga ka karanta abubuwan da suke bukata, sai ka shiga wannan portal din nasu ” www.recruitment.psc.gov.ng

Bayan ka shiga zai nuna ma inda aka rubuta “Apply” sai ka shiga, daga nan sai ka shiga “SignUp“.

Daga nan zai kawo ka inda zaka sa “First Name” “Last Name” “User Name” sannan kuma zaka kirkiri Password “Password ” “Confirm Password“. Sai ka shiga inda aka rubuta ” Sign Me Up“.

Daga nan za su turo maka sako ta Email Address, sai ka koma cikin email dinka ka duba “Inbox” ko “Spam box” za ka ga sun turo maka sako na verify da confirm , sai ka bi link din ka kasara cike bayananka a ciki, idan ka gama za su turo ma Slip dinka ta cikin email din naka.

See also  Batun kama Ado gwanja akan WakarCHASS dakuma Safara'u da Mr 442gwamnatin kano ta tsayarda matsaya.

Allah Ya ba da sa a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *