Ku daina haɗakar kwanukan cin abinci da yara, likitan hakori ya gargaɗi iyaye

Wata Likitan hakori, Dokta Idia Okoro, ta shawarci iyaye da su guji haɗakar cokali da faranti da robobin shan ruwa da ƴaƴansu domin gujewa yaɗuwar cututtuka zuwa gare su.
Okoro wanda ya ba da wannan shawarar a wata hira da kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Juma’a a Benin, ya ce hakan na iya haifar da ciwon maƙogwaro ga yara.
Ya bayyana ciwon maƙogwaro, wanda a ka fi sani da tonsillitis a matsayin kumburin maƙogwaro ta kowane gefe.
Yaa bayyana cewa cutar ta tonsillitis yawanci ƙwayoyin cuta ne na yau da kullum ke haifar da ita, amma cututtukan ƙwayoyin cuta kuma na iya zama sanadin.
“Mafi yawan kwayoyin cutar da ke haifar da tonsillitis ita ce Streptococcus pyogenes, kwayar cutar da ke haifar da strep makogwaro. Sauran nau’ikan strep da sauran ƙwayoyin cuta kuma na iya haifar da tonsillitis, ”in ji shi.
Okoro ya ce alamomin cutar tonsillitis sun haɗa da, kumburin tonsils, ciwon maƙogwaro, wahalar haɗiya da sauran su.