AMFANIN GARIN NAMIJIN GORO DA RUWAN ZAFI

Namijin goro kamar yanda Hausawa ke kira goro ne da asalin amfaninsa yana komawa ne zuwa ga magunnan gargajiya.
Yana da daci haka da kuma bauri kadan,dukda yake dacin goron baya da wata illa wacce zata hana ayi amfani da shi.

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇

A kan nemi goron daidai bukata sai a yayyanka shi gunduwa gunduwa a shanya a rana ya bushe sai a dake a maida shi gari a nemi ruwan zafi a cup na gilashi kamar yanda kuke iya gani a hoto sai a sanya cokali daya a fifita da kyau idan ya huce sai a sha,kada a saka zuma kamar yanda wasu ke yi,domin ba a cika son hada zuma da abu mai daci ba,sai a kula.

Idan kana bukatar karfin mazakuta,ka sha ko ka tamna namijin goro mintuna talatin kamin saduwa.

Idan kana bukatar ka dauki dogon lokaci a yayin jima’i ka jima baka yi inzali ba,ka tamna karamin namijin goro ko ka tafasa ka sha awa daya kamin saduwa.

Idan kana karatu baka son bacci ya daukeka,ka sami karamin namijin goro,kwara daya ka tamna ko ka sha garin nashi a ruwan zafi kamin soma karatu da dare.

Idan kana aikin tukin mota (Driving) kuma kana shakkun bacci ya daukeka,ka tamna namijin goro ko ka saka a ruwan zafi ka sha.

Idan kana fama da tarin asma sai ka jefa citta danya kwara daya ka tafasa ka sha.

Rubutawa : shafin ciwo da magani..

See also  Qalu innalillahi bakaniken ya rasa ransa ne dai dai lokacin da jack din ta ke tare da motor ya goce inda motar ta danne shi muna fatan Allah ubangiji….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *