Abin Da Ummita Ta Faɗamin Kan Saurayinta Kafin Ta Rasu”, inji Sheik Daurawa..
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cikakken bayanin magana ta tsawon mintuna 15 da su ka yi da marigayiya Ummakulsum Buhari (Ummita) ta wayar tarho game da saurayinta, mako guda kafin rasuwar ta.
Da yake bayyana abinda su ka tattauna da marigayiyar a wani faifen bidiyo da ke nuni da cewa a ɗaya daga cikin majalisin karatunsa ne, Daurawa ya ce ta kira shi ne domin neman shawara a kan mafita kan ƙudurin ta na aurar ɗan Chaina ɗin sabo da mahaifanta sun hana ta auren shi, inda yace mata;
“Na ce mata iyayenki su na da gaskiya saboda bai kamata nata ku riƙa auren wanda a ke da kokwanto a kan asalinsa,” inji Sheik Daurawa
Sai dai malamin ya ce ya bata shawarar ta gindaya wa masoyin na ta sharɗɗa biyar kafin su yi auren;
“Sharaɗi na farko shi ne a tuntuɓi hukumar shige da fice ta ƙasa don tabbatar da ko da izini ya shigo ƙasar nan. Na biyu, a yi bincike kan aikin sa a Najeriya”.
“Na uku, na san Sarkin Kano ya naɗa sarkin ‘yan Chaina a Kano, Don haka a tambayi shugaban al’ummar ƙasar ko sun san shi, yankin da ya fito da kuma abin da yake yi?”
“Na huɗu, ya kamata kuma a sanar da ofishin jakadancin cewa ɗan kasar Chaina na shirin auren ‘yar Najeriya. Na biyar kuma na umarce ta da ta sanar da Hisbah don ta kara koya masa addinin musulunci, tunda ta ce min ya musulunta”.
“Ummita ta cemin, iyayensa a ƙasar Chaina sun amince da auren, amma iyayenta sun ƙi amincewa da auren”.
“Amma na gaya mata idan kun cika waɗannan sharuɗɗa guda biyar, zan shawo kan iyayenki su yarda ki aure shi,” inji Sheik Daurawa.
Daurawa ya ƙara da cewa addinin Musulunci ya amince da aurensu, yana mai cewa addinin ya kyamaci nuna wariyar launin fata, inda ya ƙara da cewa marigayiyar ta faɗa masa cewa ɗan Chaina ɗin ya musulunta.
Sheikh Daurawa ya kuma yi kira ga hukumomin da su ke da ruwa da tsaki da su tabbatar an hukunta wanda yayi wannan ɗanyen aiki.