Tirkashi Ashe Soyayyar Yanzu Tana Ɗaya Daga Cikin Lalacewar Auren Hausawa A Yanzu
Malam Aminu Daurawa Yayi Cikakken Bayani Akan Abunda Yake Kawo Lalacewa Aure A Yanzu, Yadda Abun Yake Samo Asali Tun Daga Zance Wato Hira Da Saurayi Da Budurwa Suke Da Sunan Soyayya.
Kamar Yadda Shafin Rariya Hausa Na Facebook Suka Wallafa Zuwa Hira Da Kuma Soyayyar Da Akeyi Yanzu Yana Daya Daga Cikin Abunda Yake Kawo Lalacewar Zaman Aure A Yanzu Ga Abunda Suka Wallafa.
ZUWA ZANCE KAFIN AURE
Malam Aminu lbrahim Daurawa Yace Zance da ake yi tsakanin masu neman aure
domin su ga juna su tattauna, su gabatarwa da juna bukatar aure da kuma neman amincewa da soyayya, da fahimtar juna.
Amma a kula yadda ake zance yanzu akwai
fitsara sosai yadda ake rungume juna da taba jiki, da yin abubuwa masu muni wani lakacin har da saduwa kafin aure.
Duk wanda ta yarda wani ya taba mata jiki to ya gama ita domin ba za ta kara mutunci awajan sa ba.
Malamai sunyi sabani akan iya gurin da yaa kamata mai neman aure ya gani a jikin matar da zai auralya fadin fuska da tafin hannu.
lya shiga ta al’ada da zaman gida
Duk inda zai ja hankalin sa zuwa ga auran ta
Amfanin zuwa zance ko ganin mace domin
gabatar mata da kai, a matsayin mai neman
aure, shi ne abin da malamai suke kira
neman aure ko kuma kidbah, asali ana
neman auran mace a wajan waliyinta a
mataki na farko domin samun iznin ganin ta da tattaunawa da ita, don samun fahimta, kamar yadda Manzon Allah saw ya nemi auran Aisha a wajan mahaifinta Abubakar.
Mataki na biyu, ana iya neman auran mace
kai tsaye a wajan ta idan mai hankali ce,kamar yadda Annabi saw ya nemi auran
Ummu Salamata a wajan ta, har ta bayar da uzrin yawan yaya da shekaru da tsananin kishi, ya bata amsa da zai rike mata yayan,
shekaru kuma shima yana da su, kishin kumaa zai roki Allah ya rage mata shi, Muslim Annasaiy.
Mataki na uku Mahaifin mace ko waliyinta zai
iya gabatar da ita ga mutanan kirki, domin
sama mata miji, kamar yadda S. Umar ya
gabatar da Yarsa Hafsah ga S. Abubukar,
sannan Usman daga baya Manzon Allah saw
ya aure ta.
Da hadisin Umma
Habibah da ta nemi Manzon Allah saw ya auri
yar’uwarta, ya nuna mata baya hallata a
musulunci hada yan’uwa a igiyar aure daya a
lokaci daya.
Mataki na hudu ya halatta mace mai hankali
ta gabatar da kanta da wani mutum nagari ko
zai amince ya aure ta, kamar yadda wata
mata ta gabatar da kanta ga Manzon Allah
saw, ko zai amince ya aure ta,
Mataki na hudu wani ya na iya zama sila ko dalili wajan shige wa gaba wajan kulla alakaraure tsakanin masu neman aure kamaryadda kaulatu Bnt Hakeem ta gabatarwa da
Manzon Allah saw auran Nana Saudah bayan
wafatin mijinta.
Mataki na biyar za a iya kafa wata kungiya
mai dauke da amintattun mutane masu ilimida sanin haliyyar jama’a, su dinka zama
masu dalilin aure, duk mai neman aure mace
ko namiji sai ya je gurinsu, domin tantancewa
da shigewa gaba wajan hada aure.
Mataki na shida za a iya bude wata kafa a
Internet a bude Web site, domin wannan aiki
amma yana bukatar aiki da saka kaidoji
domin ka da a canga munufar budewar zuwa
wani abu daban.
Ku kalli Wannan Bidiyon
Toh Allah Ya Kyauta Zamu so Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Nasiha Ta Malam, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe mungode.