HOTUNA: Jaruma A Cikin Shirin Kwana Casa’in Rayyya Ta Yi Bikin Kammala Karatunta

Fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood Surayya Aminu ta kammala karatunta Kamar yadda ta wallafa wasu Hotuna a shafinta na Instagram a makon da ya gabata. 

Surayya Aminu wacce akafi sani da Rayyya a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango da gidan talabijin na Arewa24 suke haskawa, ta nuna farin cikinta na kammala karatunta. 


Sai dai lamarin ya baiwa mutane mamaki sosai musamman masu sha’awar kallon fina-finan Hausa, wasu ba su yi tunanin cewa jarumar tana yin karatu ba, sun dauka cewa tunda tana harkar finafinai ba za ta samu lokacin zuwa makaranta ba.

 

Jarumar dai ta yi wasu hotuna da abokan karatunta a ranar da suka kammala rubuta jarrabawar su ta karshe. Ita da abokan karatunta duk sun sanya fararen riguna wanda dalibai suka saba sakawa a ranar da suka kammala karatun su da ake “kira sign out”. 

Wannan yasa mabiyanta a shafin instagram suka dinga yi mata addu’a da fatan alheri tare da taya ta murnar kammala karatunta. 


Ga hotunan da jarumar ta wallafa a shafin nata Kamar haka. 

See also  Adam A Zango Na Neman Addu’ar Masoyansa ‘Yarsa Ɗaya Tilo Tana Kwance Asibiti Rai A Hannun Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *