February 25, 2024

Abu dai Kamar wasa Ashe magana harta girma domin Tsohon mijin momee gombe Adam Fasaha yana shirin Auren Jaruma Minal ahmed da akafi sani da nana Izzarso.

Idan ba’a manta ba a watanni baya da suka gabata ne Hotunan Kafin Aure na Mawaki adam fasaha da Minal ahmed suka karade Shafukan sada Zumunta, Jaruma minal Ahmed itace wacce ta fara wallafa hotunan a shafinta na Instagram sai dai kuma ba tace kala ba.  Wanda Hakan ya jefa dimbin masoyanta Cikin rudani Hakazalika daga baya shima Adam fasaha ya wallafa a shafin nasa, bayan Hotunan sun dauki hankula jama’a kuma ba tare da fahimtar abunda hakan ke nufi ba.

A karshe dai an gano cewa ba Aure ne zasuyi ba illa kawai Wata vedion waka ce zasu dauka,  To amma a yanzu kuma maganar na nema ta zama gaskiya, domin mawaki Adam fasaha ya fito ya bayyana gaskiya batun a shafinsa na Tiktok, inda har wani yake tamabayar sa cewa minal Ahmed fa gawar momee gombe ce shin zaka hadasu fada kenan?

Hakan ya baiwa Mawaki adam fasaha mamaki inda har shima ya bada amsa da cewa shin wai harun ne don na hadasu? Kalli Vedion abinda yake fada kamar haka.

See also  Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Miji da Mata da Yayansu guda biyu Sun Mutu Sanadiyyar gobara..
Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *