Anci gaba da Zagin Safara’u Kwana Casa’in Kan Cewa ta Nuna Halin Ko in Kula ga Ubangidan ta Mr442

Anci gaba da Zagin Safara’u Kwana Casa’in Kan Cewa ta Nuna Halin Ko in Kula ga Ubangidan ta Mr442
Anci gaba da Zagin Safara’u Kwana Casa’in Kan Cewa ta Nuna Halin Ko in Kula ga Ubangidan ta Mr442
Mutane nata Tsokaci wasuma harda zagi kan wata faifan vedio da Safara’u kwana Casa’in ta dora a shafinta na Tiktok inda take Cikin matukar nishadi wanda hakan yayi dai dai da bayyanar labarin cewa an kama ubangidan nata Mr442 a kasar Niger.
Hakan yasa aketa Tsokaci da zagi kan rashin nuna kulawar ta ga faruwar abun gadai vedion nan kamar haka.
A Wani Bangaren Kuma
Wani jirgin yakin sojin saman Najeriya samfurin Super Tucano ya kashe ’yan ta’addan Boko Haram 16 a yankin Banki da ke kan iyaka da Karamar Hukumar Bama a jihar Borno.
An halaka ’yan ta’addan ne a ranakun 16 da 17 ga watan Nuwamba, 2022, bayan harin sama da rundunar leken asirin sojojin saman suka yi a yankunan na kan iyaka da kasar Kamaru.
Wani kwararre a fannin yaki da tayar da kayar baya, a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, a karshen mako a Maiduguri, ya ce, “Boko Haram ta sake samun wata mummunan asara a aikin hadin gwiwa na sojojin hadin gwiwa a yankunan Banki.”
A cewarsa, ’yan ta’addan da aka kashe suna da matsuguni ne a yankunan Chongolo da Tangalanga da ke kan iyaka da Kamaru, mai tazarar kilomita 134 daga gabashin Maiduguri, babban birnin jihar.