Masha’Allah Maryam Babban Yaro itama Ta Fita daga Layin Zawarawa an Daura Aurenta a Jiya Asabar Allah bada Zaman lafiya.
Masha’Allah Maryam Babban Yaro itama Ta Fita daga Layin Zawarawa an Daura Aurenta a Jiya Asabar Allah bada Zaman lafiya.
A jiya asabar ne aka daura Auren Fitacciyar Jaruma a Masana’antar Kannywood Maryam Abubakar Gidado da akafi sani da Maryam Babban Yaro duk da cewa dai Wannan Aure ne na Sirri ba kowa yasan dashi ba sai bayan da aka gama Daurin Auren sannan ta Sanar.
Jarumar ta sanar da hakan ne ta Hanyar wallafa wata faifan bidiyo a Shafukan ta na sada Zumunta inda tayi tagging wasu daga cikin Abokanan sana’arta yan Fim.
Masoyanta da dama hade da Abokanan sana’arta sun tayata Murna wannan abun farin ciki dayazo mata Kasancewar dama an saka matan Kannywood a gaba cewa basa son yin aure kuma koda sunyi Auren basa Zama.
Tindai karshen Shekarar data gabata ne ta 2021 da kuma wannan da muke cike Aketa daura Auren Jaruman Kannywood Musamman ma Matan wanda suka hada da Yan mata da kuma Zawarawa wanda akalla an samu yan mata da Zawarawan Kusan Ashirin da Sukayi Aure acikin Karshen Shekarar 2021 zuwa 2022.
Sai dai an bayyana hakan ne a matsayin takura da Jaruman Suke sha a wajen Al’umma kan cewa sunki yin Aure wasu kuma sun bayyana cewa lokacin auren nasu yayi a yayinda wasu kuma suka bayyana cewa Harkar ta fim ce a yanzu taja baya ba kamar daba. A karshe dai muna mata Addu’a Allah basu zaman lafiya Ameen
Wannan Shine Hoton Katin bikin data wallafa nan a shafinta na Instagram.