Shuaibu Lawan Kumurci Ya Sake yin Aure, Shekaru 18 bayan rasuwar Balaraba.
Fitaccen ɗan wasan Hausa, Shuaibu Lawan Kumurci ya angwance da falleliyar matarsa ayau, bayan aƙalla shekaru goma sha takwas 18, da rasuwar tsohuwar matarsa Balaraba.
Balaraba ta rasu ne cikin shekarar 2003 bayan da ta gamu da iftila’in haɗarin mota a hanyar Jos.
Ayau ne dai Kumurcin ya angwance.