Naziru Sarkin Waka har yanzu bai cika mun Alkawarin daya dauka ba cewar wanda zai siyar da kanshi akan N20

A shekarar 2021 ne wani matashi daga jihar Kaduna yazo Kano nan Unguwar Zoo Road yana neman wanda zai siye shi akan farashin miliyan 20,kafin daga bisani yace yana son Naziru Sarkin Waka ya siye Shi,a lokacin yaron ya bayyanawa duniya cewa ya yarda a siye shi in har baza’a sabawa Allah dashi ba zai zama kamar bawa ga duk wanda ya siye shi.

Sai dai daga bisani aka mika shi ga ofishin Hisbah mafi kusa, daga nan ne aka hadashi da Naziru Sarkin Waka din har yayi mishi wani Alkawari.

Sai dai a jiya Matashin ya wallafa a shafinsa na Tiktok cewa shifa har yanzu yaji shiru ba’a cika mishi Alkawarin ba, daga karshe har yake rokon ko da Keken dinki ne Nazirun ya siya mishi shi ya hakura da daya Alkawarin.

See also  Inna Lillahi! Wata Amarya ta rasu ana gobe daurin Auren ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *