Wani Lokacin Ƴan Iskan Maza Sunfi Iya Soyayya – Fatima Umar

Cikin wani yanayi mai kama da abin dariya, wata budurwa ma’abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna Fatima Umar ta bayyana irin mazan da su ka fi iya soyayya.

Yayin da mata da dama ke neman maza natsatstsu da hankali, ita ra’ayinta dangane da maza wadanda su ka fi lakantar soyayya yasha bamban da na ragowar al’umma gamagari.

Budurwar wacce tayi wallafar tare da hadawa da wani hotonta wanda ta dau cikin yanayi mai kyau, ta bayyana cewa maza ƴan iska sun fi iya soyayya.

A cewar Fatima, wani lokacin maza ƴan iska sun fi iya soyayya maimakon maza masu natsuwa.

Tabbas wannan wallafar ta dauki hankali kwarai, inda wasu ke ganin gaskiya maganarta, wasu kuma na ganin akasin haka.

To sai da dama dinga baikonta kan hakan, baya ga bayyana irin raayinsu kan batun nata.

Cikin wani labarin na daban, ana zargin wata mata mai suna Yetunde Folorunsho ta kashe kanta ta hanyar shan gubar maganin ƙwari domin ta hana mijin ta mai suna Dare Araoje ƙara aure.

Dailytrust ta wallafa cewa wannan lamari dai ya faru ne a garin Ilorin na jihar kwara inda matar wacce take da ƴaƴa biyu tare da mijin ta suke zaune.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na jihar kwara Ajayi Okasanmi ya shaidawa manema labarai cewa binciken da suka gudanar akan gawar matar ya tabbatar da cewa lallai ta sha maganin ƙwarin nan ne da ake kira da ‘sniper’ wanda shine yayi ajalin nata.

Matar, wacce tayi digirin ta a bangaren nazarin yaruka, wacce kuma ƴar asalin jihar Osun ce ta mutu ne a lokacin da ake kan hanyar kaita asibitin gwamanti dake garin Ilorin.

See also  Yanzu yansu Rikici Ya Barke Tsakanin Rarara Da Daushe Da Aisha Humaira Akan Siyasar Kano…….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *