Innalilahi wa’inna Ilaihi raji’un Yadda Wasu yan gida daya suka rasa Ransu…

Innalilahi wa’inna Ilaihi raji’un Yadda Wasu yan gida daya suka rasa Ransu…

Hakika wannan Rashwar bayin Allah ta dagawa mutane hankali musamman yan uwan su da suka kaiwa ziyara.

A safiyar yau ne muke samun labarain rasuwar wasu yan gida daya ta hanyar hadarin mota, Allah ya karbi rayiwar su akan hanyarsu ta zuwa jihar Jigawa.

Abdul Gajo Shi da ɗan uwansa Liman Gajo a hanyansu ta zuwa Jigawa don halarta Jana’izar kawun su Alhaji Habibu Gajo Yalleman.

Dama duk mai rai mamaci ne, Muna rokon allah ya ya gafarta musu mu kuma idan tamu tazo kasa mu cika da imani.

Yunwa ce ta yi ajalin ɗan uwan Dahir. Yanzu haka kuma akwai ‘yan uwansa mata biyu da ke kwance rai-kwakwai mutu-kwakwai saboda rashin abinci mai gina jiki.

Wakilin BBC Andrew Harding ya koma Baidoa domin sake ziyartar iyalan da fari ya raba da matsugunansu irin sa mafi tsanani a cikin shekaru 40 a Somalia, yayin da mahukunta ke kira ga ƙasashen duniya su ayyana dokar ta-baci kan yanayin da ake ciki a ƙasar.

Gargadi: Wannan makala na dauke da hotunan da ka iya tayar da hankalin mai karatu

Dahir, mai shekara 11, yana ratsawa tsakanin bukkoki da ke gefen dajin Baidoa, zuwa ga makarantarsu ta kwano da aka gina a kusa da wata babbar hanya.

Yana sanye da tufafi ƙwalli guda da yake da shi wato wando da riga, sannan yana riƙe da littafinsa.

Malamin makarantar, Abdullah Ahmed, mai shekara 29, ya rubuta sunayen ranaku a jikin allo, yayin da Dahir da abokan karatunsu kusan 50, ke karantu: ‘Saturday, Sunday, Monday…’.

Kusan ‘yan daƙiƙoki, kana iya jin karsashin yaran da shauƙi a cikin karatunsu, sai dai lokaci kaɗan sai suka soma hamma da tari – alamar yunwa da cutar da ke addabarsu a Baidoa, yankin da ya kasance mafaka ta tsawon watanni ga daruruwa ko dubban fararen-hula da fari irin sa mafi muni cikin shekaru 40 ya ɗaiɗaita ‘yan Somalia.

“Ina ganin kusan yara 30 ba su yi karin-kumallo ba. Wani lokaci suna zuwa wajena kai-tsaye su faɗa mun cewa suna jin yunwa,” a cewar Mista Ahmed. ” Ba sa iya samun nutsuwa, ko fitowa aji.”

Mako shida baya, a wata ziyara da muka kai yankin kudancin Somalia, Dahir ya zauna yana kuka, kusa da mahaifiyarsu Fatuma, a wajen bukkar da yake zaune tare da iyayensa da kuma ‘yan uwa.

Kwanaki kafin wannan lokaci, kanensa, Salat, ya mutu saboda tsananin yunwa a hanyarsu ta zuwa Baidoa da fari ya kora galibin ‘yan kasar.

An yi jana’izar Salat a wani yanki mai ɗan tazara. Yanzu haka kabarinsa zagaye yake da bukkokin sabbin mutane da suka isa yankin.

“Ina cikin damuwa sosai kan ‘yar uwata. Ina yi musu wanki. Ina kuma wanke musu fuska,” a cewar Dahir, yana kallon kanwarsa mai shekara shida Mariam, da ke tsananin tari da korafin cewa kanta na ciwo, da kuma kanwarsa mai shekara hudu, Malyun da ke zaune idonta ya yi zuru-zuru a cinyar mahaifiyarsu.

“Cikinta ya yi zafi. Ina tunani tana da ƙyanda. Babu mamaki dukkaninsu na ɗauke da ƙyanda,” a cewar Fatuma, hannunta dafe a goshin Malyun.

Ƙyanda da cutar sanyi ta limoniya sun yi illa sosai a watannin baya-bayan nan, tare da kashe kananan yara da garkuwar jikunsu ta yi rauni saboda rashin abinci mai gina jiki.

A wani asibitin wucin-gadi da ke tsakiyar Baidoa, likitoci da jami’an jinya na zagaye daga wannan gado zuwa wancan, yana sanya ruwa da allurai ga jarirai, da sa musu iskar shakar numfashi ta hanci.

Yara da dama hannunsu da kafufuwansu sun yi duhu sannan kuraje sun feso a ko ina – kamar an ƙona su – alamar da ke nuna yaro na cikin tsananin yunwa na tsawon lokaci.

“Mun karɓi wasu ƙarin tallafi. Amma dai ba su wadatar ba,” a cewar Abdullahi Yusuf, shugaban asibitin.

“Duniya ta sanya ido kan farin Somalia a wannan lokaci. Muna karbar baƙi da ke kawo tallafi daga waje. Amma hakan ba yana nufin muna samun isashen tallafi ba ne. Ammam muna fatan a kawo mana ƙarin dauki. Yanayi ne mai tsanani.”

Makonni shida baya, ya bayyana batun a matsayin mai ‘razanarwa’.

A yau ya ce an samu ragin mutanen da ake kwantarwa amma a ganinsa hakan baya rasa nasaba da ruwan sama da ya lalata hanyoyi da kuma tilastawa wasu iyalai zama su mayar da hankali kan batun shuka maimakon kwaso yaya zuwa asibiti.

Yanayin na sake ‘munanan’

Can a sansanin, Fatuma ta ciko jarka da ruwa daga famfo. Dahir ya fito daga bukkarsu domin ya taimaka mata da gyaran gida, yayin da ‘ya’yanta mata biyu ke kwance a cikin bukkar.

“Ɗana na taimaka min sosai. Yana yin duk mai yiwuwa domin taimaka wa kannensa mata,” a cewar Fatuma.

Lokacin da take tafasa ruwa, wayarta ta yi kara. Mijinta, mai shekara 60 Adan Nur, na kiranta daga kauyensu da ake kwashe kwanaki uku kafin a isa, yankin da ‘yan ta’addan IS masu aiki da al-Shabab ke iko da shi.

“Ya ce ya yi shukar hatsi. Yana nan lafiya. Zai dawo nan ba da jimawa ba. Amma mun rasa dukkanin dabobbinmu. Babu ta yadda za mu rayu da wannan hatsi kawai, don haka dole na ci gaba da zama a nan. Wannan yanayi na rayuwar ya wuce,” a cewar Fatuma bayan kammala wayar.

Shawarar da ta yanke kusan ta yi daidai da gargaɗin masana, da ke cewa ruwan sama da ake yi ba zai wadatar ba, kamar dai watanni huɗu baya – ana iya ganin yadda shukoki suka yi kore shar amma kuma babu wani sauyi ko tasiri kan matsalolin yunwa ƙasar.

“Yanayin na sake tsanani. Mutane da dama na zuwa nan domin neman abinci, tsaro da ruwa. Sannan yara da yawa na mutuwa saboda yunwa. Muna rokon gwamnati da kasashen duniya su duba wannan lamari na yunwa,” a cewar magajin garin Baidoa Abdullah Watiin, da ke fitowa daga wajen taron da al’umma yankin suka shirya.

A cikin ɗakin taron, wani janar din soja ya gargaɗi mutanen yankin kan shuka, saboda barazanar al-Shabab, yana mai ce musu su ke taka-tsantsan da abubuwan fashewa ko harin ba-zata.

Dakarun gwammatin Somalia da mayaƙa na sa ran kai sabbin farmaki domin samun nasarori a yankunan arewa, sai dai hakan na sake nuna irin barazanar da ake ciki na iya kai wa ga wasu yankunan karkara da fari ya yi wa mumunan illa.

Fatuma ta kwantar da ‘ya’yanta biyu mata mara lafiya – Mariam da Malyun mai shekara hudu – a kan shimfidar bargo mai dauke dauɗa a cikin bukkarsu.

Tayin a kai su asibiti bai yiwu ba saboda wasu dalilai da magunguna gargajiya da suke yi. Fatuma cikin yanayi na damuwa, ta kwanta tare da raɓawa jikin ‘ya’yanta mata.

See also  😭😭😭 Innalillahi wainna ilaihi Raju un yanzu yanzu baban cinaidu yayi zazzafan martani zuwaga dauda kahuta rarara yanzu yanzu kalli wannan video domin kagani da idonka….

Add a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *