Boka Ya Dirka Wa Wata Mata Ciki_Bayan Ya Yaudareta Akan Sahihen Magungunansa’A kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama
wani boka da ake zargi da yi wa wata mata ciki bayan ta je wajensa neman magani.

Bokan mai suna Muhammad Mansur, mazaunin Karamar Hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano, an kama shi ne bayan matar da ba a bayyana sunanta ba, ta kai kara tana neman a bi mata hakkinta akan cikinsa wata bakawai da take dauke da shi.

Rahotanni daga garin na nuna cewa bokan ya yi fice wajen yaudarar mata, ciki har da matan aure yana kwanciya da su.

Bokan na yaudarar mata ne ta hanyar shaida masu cewa, idan suka kwanta da shi zai ba su maganin da zai hana a yi masu kishiya da kuma mallakar miji.

Matar ta fada wa Hisbah cewa lokacin da ta je neman maganin wajen bokan ya shaida mata cewa ba zai yiwu ba, sai sun kwana tare.

A cewar ta, mutumin ya jima yana neman saduwa da ita, idan sun je wajensa tare da mahaifiyarta, amma bai yi nasara ba, har sai lokacin da ta ziyarce shi ita kadai.

Bokan, Muhammad Mansur ya amsa wannan laifi, sai dai ya ce aikin shaiɗan ne.

Shugaban rundunar Hisbah reshen Karamar Hukumar, Ustaz Kabiru Musa Dawakiji, ya ce za su ci gaba da bincike domin daukan mataki.

Irin wannan matsalar dai ta zama ruwan dare game duniya a tsakanin bokaye da ‘yan tsubbu a kusan ko’ina a fadin kasar nan, kamar yadda wasu masharhanta suka bayyana.

See also  Cikakken Tarihin Nura Mustapha Waye Director IZZAR SO

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *