Budurwa Ta dawo Najeriya Daga Dubai Saboda Bikin Kawarta Sai Kuma Ta Tarar Saurayinta Ne

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya wacce ta yo tattaki daga Dubai ta hadaddiyar daular larabawa ta gano cewa aminiyarta tayi mata kwacen saurayi.

Cikin wani bidiyo da budurwar ta wallafa a TikTok a ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamva, aminiyarta zata yi aure sai ta yanke shawarar halartan baikonta.

Amma cikin mamaki, Princess tace da ta isa wajen bikin baikon, sai ta gano cewa mijin saurayinta ne.

Ku Karanta WannanYadda Likitoci Suka Ciro Ƴan Tayi 8 A Cikin Wata Jaririya

Ta ci gaba da cewar aminiyar tata har ta haifawa saurayin nata yaro dan shekaru biyu.

Labarin ya kaɗa hantar cikin mutane da dama domin abun akwai al’ajabi, inda wasu suka kira ta da makaryaciya.

Princess ta wallafa bidiyon lokacin da take barin filin jirgin sama zuwa Najeriya.

To sai dai mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari mai cike da sarkakiya.

Hakan ba sabon abu bane musanman a Najeriya, budurwa tayi wuff da saurayin kawarta, haka suna bangaren maza ana iya samun hakan.

A baya bayan nan an samu irin hakan da dama musanman na Najeriya, inda wasu manya suka dinga yin wuff da ƴan matan ƴaƴansu.

See also  Zazzafan martani Abdullahi umar ganduje akan wannan rusau kalli wannan video domin kagani da idonka yanzu yanzu innalillahi wainna ilaihi Raju un karka bari abaka labari…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *