Hotunan Yadda Aka Daura Auren Jarumi Abale Na Shirin Aduniya

A yau Juma’a ne aka daura auren fitaccen Jarumi a Masana’antar shirya Finafinan Hausa watau Adam Abdullahi Adam wanda akafi sani da Abale acikin shiri me dogon Zango a duniya.

Wannan batun daurin Aure yazo ne a matsayin bazata domin harma wasu daga cikin Abokanan sana’arsa basu san da Maganar saka bikin ba, sai dai kawai sukaga katin gayyata ya bayyana wanda kuma ayau Juma’a 27 ga watan January na shekarar 2023 aka daura auren.

Duk da cewa har yanzu angon bai bayyana Hotunan sa tare da amaryarsa ba, amma an hango Fuskokin wasu manyan jarumai na Masana’antar ta Kannywood awurin Shagalin Bikin, kamar irinsu ali nuhu, yakubu Mohammad, Shuaibu Lilisco, Abubakar Bashir Maishadda da sauran su

See also  VIDEO: Zanga-Zangar Lumana Kan Sai Hukunta Alhasan Ado Doguwa Daga Ƙaramar Hukumar Doguwa Kano State….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *