Yan sanda sun cafke Jarumar Tiktok murja Ibrahim Kunya
Yan sanda sun cafke Jarumar Tiktok murja Ibrahim Kunya
Daga freedom redio
Rundunar Ƴan Sandan jihar Kano ta kama fitacciyar mai barkwancin nan ta #TikTok Murja Ibrahim Kunya.
Koda ya ke Ƴan sandan ba su yi ƙarin bayani ba, amma idan zaku iya tunawa a shekarar da ta gabata ne wani lauya ya shigar da ƙorafi inda yake neman da a binciki Murja da wasu fitattun mawaƙa da masu amfani da TikTok kan zargin ɓata tarbiyya.
An kama Murjar ne yayin da take tsaka da shirye-shiryen shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Ƙarin bayani zai zo nan gaba.