Dalilan Dasuke Lalata Tarbiyyar Yaran Hausawa A Yanzu
Innalillahi Gaskiya Wannan Ba Tarbiyya hausawa Bace Kalli Yadda Amarya Take Rawar Iskanci Agaban Kowa
YADUWAR ZINA ACIKIN AL’UMMAH.
WAYOYIN SALULA: Wayoyin salula suna taka mummunar rawa cikin yaduwar fasadi da lalacewar tarbiyar AL’UMMAH. Musamman ta bangaren HOTUNA da VIDIYO NA BATSA da recording na kalmomin batsa wanda matasa maza da mata suke turawa a wayoyinsu. Yara Qanana sukan kalli hotunan yadda ake jima’i. Daga nan kuma sai shedanci ya shiga zukatansu su fara tunanin hanyoyin da zasu bi su rika samun biyan bukatarsu, alhali da can irin wannan tunanin bai taba shiga kwakwalwarsu ba.
YADUWAR FINAFINAI: Yaduwar Finafinaina waje da kuma na gida shima ya taimaka wajen watsewar al’amura. Ba don komai ba, idan ka lura da yadda rayuwar Matan hausawa take acikin shekarun 1980 zuwa 2000 zaka ga ba daidai take da wacce mukeyi yanzu ba.
Tun daga salon dinkuna da suke sawa, da kuma yadda suke kula da tarbiyar yaransu, da kuma tarbiyarsu ga mazajen aurensu.
WURAREN PARTY: idan akayi la’akari da yadda kullum harkokin party suke kara bunkasa a tsakanin matasa da kuma irin watsewar da akeyi awajen, lallai za’a fahimci cewar harkar party tana daga miyagun Abubuwan dake addabar tarbiyar al’umma. Ana haduwa maza da mata awajen kuma ana aikata haramtattun abubuwa iri-iri wadanda ba sai na lissafa ba.
DON HAKA ya zama wajibi a matsayin ka/ki na uwa da uba Ku tsaya tsayin daka wajen lurada tarbiyar yaranku, domin ALLAHU SWT cewa yayi “Ku kare kawunanku da na iyalanku daga shiga wuta” wallahi ALLAH zai tsaida kai ya tambaye ka ya ka tafiyar da amanar da ya baka? Kuma sai ka amsa.
ALLAH ya shiryar da zuri’ar musulmai baki daya
Wasu daga cikin dalilan da suka sa wannan bala’i ta zina ta yawaita cikin AL’UMMAH.
- TALLE: Mafiya yawan yara matan dake yawon talle a cikin kasuwanni, Garejoji, Tashoshin mota, da Unguwanni suna cikin hatsarin afkawa cikin wannan mummunar dabi’a. Ba don komai ba sai saboda yadda kullum zasu rika jin kalamai na batsa da kuma miyagun wasanni irin na batsa da suke samu daga shashashun samari da kuma tsofaffin yan tasha.