May 18, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/hurvr/public_html/wp-content/themes/chromenews/lib/breadcrumb-trail/inc/breadcrumbs.php on line 253

Shahararren ɗan ƙwallon ƙafan Nageriya kúma Kaftin ɗin ƙungiyar Super Eagles, Captain Ahmed Musa MON ya kai ziyarar jaje da ta’aziyya ga iyayen matashin nan mai wasan barkwanci, Kamal Aboki wanda Allah Ya Yi wa rasuwa a ƴan kwanakin baya Sakamakón hatsarín Møta.

A ya yin ta’aziyyar, Captain Ahmad Musa ya ga gidan da Kamal ɗin ya fara ginawa iyayensa bai gama ba Allah Ya karɓi rayuwarsa. Yanzu Ahmad Musa ɗin ya ɗauki nauyin kammala musu ginin gidan gaba ɗaya.

Allah Ya sakawa Captain Ahmad Musa da Alkhairi haƙiƙa shi ɗin abin alfahari ne ya yi abin a yaba. Kuma dama ɗabi’arsa ce taimako da jin ƙan al’umma gami da ba da tallafin jari ga masu ƙaramin ƙarfi. Allah Ya ƙara yalwata arziƙinsa Ya saka masa da alkhairi. :

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *