June 12, 2024

Babban jarumi kuma mawaki Garzali Miko yayi wani bidiyo tare da babbar jarumar rawar waka wato Rakiya Musa yar asakin kasar nijar wacce wannan hakar ta dawo da ita kasar nijeriya.Wannan bidiyo da sukayi yana taba jikinta wanda mutane sukayi ta magana kan bai dace ba ko bai duba Allah ya haramta hakan ba yakamata ya duba matar shi daya bari a gida domin baza taji dadi ba ko bata gani da kanta ba yana hana ruwa gudu zasu je domin nuna mata.Ana cikin wannan sai kuma ga wani tsohon bidiyon nasu shi da jaruma Rakiya suna rawa a gidan gala har ya dauki hannunsa ya daura a kirjinta. Wanda wannan bidiyo yafi fusata mutane matuka kan bidiyon farko.Duk zagin da ake yiwa wannan jarumai a cikin haryanzu babu wanda yace uffan game da zaginsu da tsinuwa da ake masu. Daya daga cikin masoyan jarumi garzaki miko ya bashi shawara ya fara da cewa “Shiyasa ake so mutum tun daga kutucuyar shi har zuwa girmansa ya aikata abun alheri kodan saboda yaranshi.Kaga kila kai ka manta da wannan bidiyo saboda kayi shi da dadewa sannan kuma lokacin babu tunanin aure a gabanka kuma babu tunanin ya yaranka zasu ji idan suka tashi ana nuna mahaifinsu ne anan yake taba kirjin wasu matan a gidan gala.Da kayi wannan tunanin a lokacin bazaka aikata ba amma gashi har lokaci ya fara kure maka kayi aure harka haihu yanzu yadda wannan bidiyon ya dawo yana yawo ana zaginka haka idan yaranka su girma za’a kara dawowa dashi ana ci masu mutunci dashi.Har yanzu akwai sauran damar ka gyara idan kaga kanason ka bawa yaranka rayuwa mutunci da daraja a duniya da lahira.” Anan wannan masoyin nashi ya tsaya sannan yayi mashi fatan alheri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *