April 16, 2024

Abubuwan Da Suke Kawo Hooking A Wayar Android, Da Kuma Yadda Zaka Magance Shi.

Barkanku da zuwa wannan website mai suna Hausatiktok. Com.Ng.

Yau na zo muku da wani sabon sarasi a kan wasu matsaloli da ake samu lokita-lokuta a wayar Android.

Karanta ta wannan: Har Yanzu Ni Masoyin Buhari Ne – In ji Fasinjan da ya kubuta daga hannu ‘Yan ta’adda.

 

Matane suna korafin cewa wasu lokuta suna cikin amfani da wayarsu ta Android sai su ga tana kakkamewa, wato tana hooking.

A wasu lokutan kuma sai ga ka wayar Idan an shiga wani App din sai ta kame.
Misali, wata wayar Android din musamman ma GN Phone a wasu lokutan sai ka ga Idan ka shiga File Manager tana dan kamewa. Amma kuma sai ka ga ko’ina ka shiga a wayar ba ta kame mutukar ba ka shiga File Manager ba, wata kuma takan zabi App ne wanda inde ka shiga to sai ta kame.Hakan na faruwa ne saboda wasu dalilai.

 

Karanata wannan: Ba Za Mu Iya Ciyo Bashin N 11Trn Ba Saboda Yajin Aikin Asuu -Festus Keyamo

DALILIN DA KE SA ANDROID HOOKING

  • Rashin Space a kan waya: ( Phone main memory): Wannan na daga cikin manyan abubuwan da suke sa wayar Android kamewa. In dai ya kasance main phone merory ba space to kwa za ka ga wayar tana kakkamewa.  Misali, Idan Android Phone tana 8Gb space, ka da ka cike duk space din wayar, kamata ya yi a ce akalla kana da available space na 2Gb space.          Wasu lokutan ma sai ka ga idan space din wayar ya yi kasa da 1Gb, wayar ba za ta ba ka damar Install a new Applications ba. Kawai za ka ga ta nuna ma “Installed” amma kuma idan ka duba ba ya kan wayar.
  • Lalacaccen Memory Card: Idan Memory Card a wayar Android ya lalace yana sa ka ga idan kana amfani da wayar tana kakkamewa. Misali Wani memory card din sai ka ga idan ka tura masa music (songs) kalau za ka yana playing songs din, amma idan ka tura masa Videos sai ka ga yana kakkamewa ko kuma ka ga ba ya bada damar ka yi Skipp na bidiyon domin ganin inda kake so. To Idan Memory Card ya fara ba da irin wannan matsalar yana sa waya tana kakkamewa.
  • Karanci RAM na wayar Android: Karancin RAM a wayar Android ma yana sa ka ga idan kana amfani da ita wasu lokutan tana kakkamewa, musamman ma idan ka fiye yin minemize daga wannan application zuwa wancan.                                    Amma an fi samu irin wannan matsalar a wayar da take da kasa da 1Gb RAM ko 1Gb RAM, wani lokacin mai 2Gb RAM ma tana yi idan ka fiye shige-shige da wayar.
  • Takurawa Battery da ciko: Android phones din da suke dauke da removable battery; wato battery da ake iya cire shi daga kan waya, a wasu lokutan suna kakkamewa idan aka takurawa batirin da cikon takarda ko kwali, musamman ma idan batirin ba ya setuwa sai an masa cikon, to idan cikon ya yi yawa yakan sa ka ga wayar Android din tana kakkamewa.

Karanta wannan: Yadda Za ka Cike aikin Dan Sanda Da Wayarka Cikin Sauki

Wandannan kadan kenan daga cikin abubuwan da suke sa wayar Android kamewa. Ku kasance da wannan website namu mai suna Hausatiktok. Com.Ng domin kowo muku bayanan da za ku gyara wayoyinku da kuma sim cards in a legal way. Na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *