May 20, 2024

Allah Sarki Duniya, Kalli Yadda Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 7 Yan gida daya a Jihar Taraba bayan Sunyi garkuwa dasu

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Yan Bindiga Sun Kashe Iyalan Sarkin Mutum biyu harsu Bakwai a karamar Hukumar gasool ta Jihar Taraba Bayan Sun Yi Garkuwa Da Su.

Mai Martaba Sarkin Mutum Biyu dake karamar hukumar Gassol a jihar Taraba, ya jagoaranci zuwa makabarta domin halartar jana’izan iyalansa da ‘yan ta’adda suka halaka bayan sun yi garkuwa da su.

A ranar 19/1/2023 ne masu garkuwa da mutane suka kutsa cikin gidan Sarkin garin na Mutum-biyu inda suka yi garkuwa da matansa biyu da yaran sa su biyar, inda suka nemi fansar naira milyan dari da sittin daga wajan mahaifinsu, amma hakan bata samu ba.

Hakan Yasa suka buda masu Wuta gaba dayan su suka yi musu kisan gilla, Kamar dai yadda aka sani rashin tsaro a Nigeria yana daya daga cikin manyan kalubale da yake addabar al’umma a wannan kasa musamman ma Arewacin Nigeria.

Wanda kuma har yanzu babu wani tabbacin tsaro ko dakile faruwar hakan daga hukumomin kasar, hakan yan Bindiga a kullum sukecin karansu ba babbaka…… To a karshe muna yi masu Addu’a Allah ubangiji yaji kansu da rahama idan tamu tazo yasa mu cika da kyau da imani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *