April 16, 2024

Wata mata kenan data haifi jaririyar ta ta farko bayan Shekaru goma sha hudu tana jiran Haihuwa bata samu ba, harma ta yanke kauna da samun haihuwar.

Acikin shekarun da tayi tana jira ta samu barin ciki har sau takwas wanda hakan ya matukar jefata acikin Mawuyacin hali, har takaiga ta fara hakura da maganar Haihuwa a Rayuwar ta.

Amma da yake Allah mai jin kan bawansa ne Allah ya bata haihuwa a lokacin da bata tunanin hakan, akwai mutane da dama masu fama da irin wannan matsalar ta rashin Haihuwa waccen wasu harma sai kaga tsufa ya kamasu Amma basu samu haihuwar ba. Sai daga karshe kuma Allah ya basu alokacin da basu tsammani


A karshe dai wannan mata tayi matukar godiya ga ubangiji daya faranta mata rai da abinda ta dade tana jira a Rayuwar ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *