April 23, 2024

An Kama Wani Katon Gardi Mai Shigar Mata Yana Shiga Makarantar Yan Mata Domin Ya Lallatse Su

Ga Bidiyon mutumcin

MUSULUNCI SHINE ADDININ DA YA DAUKAKA DARAJAR MACE

Kafin karni na 17 yahudu da nasara ba su dauki mace a matsayin halittar mutane ba, don haka ba su dauketa da daraja ba, sun bautar da mata, sun wulakanta su

Shiyasa manyan sarakunan Rumawa suke shirya wata irin gasa a wancan lokacin, suna sa a tara mata tsirara su zabi na zaba, shine abinda aka sani a yau “zaben sarauniyar kyawawa”

A Kasar Ingila har wajejen shekarun 70s ba su dena banbance tsakanin albashin mace da na miji ba, sun daukaka darajar albashin maza akan na mata, saboda yadda suka taso suka ga kakanninsu sunayi akan rashin daraja ‘ya mace

Turawan da wawayen Musulmai ‘yan boko aqeedah suke kwaikwayonsu a yau, abinda suka dauki mace itace wata haja da za’a kwanta a ji dadi da ita, sannan ayi talle da ita, sannan a jefa sharri da tarko da ita

Akwai wani bature tsohon mawaki ‘dan Amurka na manta sunansa, shi cewa yayi da zai samu dama da ya kwanta da matan duniya gaba daya, saboda yadda ba su dauki mata da daraja ba, yau su kwanta da wannan su jefar, gobe su kwanta da wancan, haka suke rayuwar kamar garken awaki

Jan gwarzon Musulunci mutumin Kasar Iraqi wanda ake kira da Salahudden Al-ayyubiy ya kafa daular Musulunci a Kasar Egypt tayi tasiri sosai, wanda ya taba jagorantar rundinar Musulmi suka kwato Qudus daga hannun yahudawa a karni na 18

Salahudden yace, idan ana so a ruguza kasa cikin sauki ba tare da yaki na makami ba, hanyar shine barin mata suyi yawo tsirara tare da yaduwar zinace-zinace

Don haka duk lokacin da aka fara kiran mata su fita babu hijabi makirci ne, halaka mu ake so ayi, ance farkon fitinar da ta fadawa yahudawa ta afka musu ne ta sanadin mata

Da jimawa, akwai manyan rikakkun ‘yan boko aqeedah da na sani a wannan dandali na facebook wadanda suke bada fatawar mata su cire hijabin su, suyi hoto babu hijabi su yada a media ba laifi bane, amma ban taba ganin daya daga cikin ‘yan boko aqeedar ya saka hoton matarshi ko ‘yarshi babu hijabi ba, da hijabin ma basu taba sawa ba

Sun killace matansu a gida, sun boye su don su kare mutuncinsu, sunzo suna kokarin halakar da matansu wasu da ‘ya’yan wasu, suna kaisu ga halaka da lalacewa, wannan tsananin mugunta ne da zalunci da cin amana, hakika babu wani mutumin kirki da zai ji dadi ana tallata matarsa ko ‘yarsa babu hijabi babu sutura na mutunci

Na san halin da mata suke fuskanta a kafofin sada zumunta saboda harin da mazinata suke kai musu, akwai matan da na san kyakkyawan niyya yake kawo su kafofin sada zumunta, don su boye kansu sai su bude account da sunan ‘ya’yan su maza ko kannensu maza, to ina kuwa ga wadanda suke bude account da sunansu na mata suna yada hotunansu babu hijabi? Allah ne kadai Ya san adadin lalatattun maza da suke kaddamar musu da mummunan hari

Na taba wallafa wani rubutu a kwanakin baya, nace matan da suke fitar da hotunansu a kafofin sada zumunta babu hijabi hoto mai bayyana sura na sha’awa suna yi ne don abubuwa kamar haka:

Damfara ta neman kudin

Sunyi kwantai suna neman mijin aure

Karuwanci suna neman kwastomomi

Jahilci da rashin sanin illar yada hoto a media babu hijabi

Na farko, damfara: Iaki tayi sana’a, sai ta koma zuwa studio ana daukarta a hoto ayi editing a photoshop application ayi mata kwalliya a tura mata a waya, daga nan sai ta tura a media tana damfarar gidadawa suna tura mata kudi, irin wannan damfarar har maza ‘yan daudu ‘yan Luwadi masu amfani da sunan mata na yi

Na biyu sunyi kwantai: Idan mace ta rasa mijin aure a garinsu ko unguwarsu sai ta dawo media, kuma sai aka lalata tunaninta cewa idan ta fara bayyana surar jikinta zata iya dacewa da mijin aure, alhali duk mata masu irin wannan wallahi kashi 99 cikin 100 dinsu ba su cika dacewa da mazan kwarai ba, saboda mutanen kirki ba su cika damuwa da irin wadannan matan ba

Karuwanci suna neman Kwastomomi: Wani Littafi da na rubutu mai taken “Rayuwar karuwai cikin sirri” na gutsuro muku shi shekarar 2020 da ta gabata, na fadi har yadda irin wadannan modern karuwai suke dana tarko wa manyan ‘yan siyasa da sarakuna, suna mayar da su ATM Machine na cirar kudi

Jahilci da rashin sanin illar yada hoto a media yana daga cikin abinda yasa wasu matan ke fitar da hotunansu babu hijabi, bata san cewa duk abinda ya hau internet zai iya tabbata har karshen duniya ba, watakila cikin zuriyar da zata haifa akwai babban Malami, illar zai shafi har jikokinta, masu gudanar da shafukan batsa suna daukar irin wadanann hotuna na mata suna editing wajen tallata hajarsu

Wani ‘dan Luwadi ya taba daukar hoton wata matar aure ya bude group Whatsapp na Luwadi da Madigo, binciken mu ya kai gareshi, da muka fitar da abin sako sai da ya riski matar da mijinta, tace bata san yadda akayi hotonta ya fita ba, mafi yawancin hotuna na mata da kuke gani ana yadawa a kafofin sada zumunta ‘yan daudu ne ke gudanar da su, musamman a shafuka na ‘yan Luwadi da Madigo

Ina jawo hankalin mutanen mu, ku dena yadda hodar acuci maza ta yaudareku, yawancinsu munana ne, da zaka gansu a zahiri babu kwalliya sai kun gudu, abu mai kyau da daraja sai ansha wahala ake samunsa

Ke kuma baiwar Allah, ki sani duk wani abu mai mutunci da daraja boyeshi ake a cikin mutunci, idan wani ‘dan boko aqeedah da ya zugaki ki fitar da hoto kice masa ya fara fitar da hoton matarsa ko na kanwarsa

Kamar yadda wata baiwar Allah tace, zasuyi ta zuga ku, suna yabonku idan kunyi shigar banza, amma da yawansu ko kyauta akace za’a aura muku su ba zasu tabba yadda ba, shi mazinaci ‘dan boko aqeedah yafi kowa kyamar ya auri ko da wacce yake zargin ballagaza ce mazinaciya, saboda duk wani mai hankali yana son abu mai daraja da mutunci

Yaa Allah Ka tsare mana imanin mu, Ka kare mana ‘yan uwa Musulmi daga sharrin fitinar karshen zamani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *