Ango Yayi Wuff Da Babbar Kawa Bayan Amarya Ta Bashi Ciwon Kai Ranar Daurin Aure

A wani labari da muke samu ya shiada mana cewa al’ummar garin Mararraban Guruku da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nassarawa sun wayi gari da abin mamaki a ranar Asabar da ta gabata bayan wata budurwa mai suna Hafsat Danladi ta bukaci a dakatar da daurin aurenta da wani saurayi.

Sai dai ana cikin haka sai daya daga cikin kawayenta da suka zo gidan bikin mai suna Zainab Sa’id ta gabatar da kanta ga saurayin tare da bukatar a yi auren da ita.

Amihad.com ta samu labarin cewa daurin auren wanda da farko aka yi niyyar yi bayan Sallar Azahar, an bukaci jama’a su yi hakuri su sake komawa masallaci bayan Sallar la’asar, inda aka daura auren a lokacin bayan an tuntubi waliyyan sabuwar amaryar da kuma yi mata gwaje-gwajen kiwon lafiya.

Wani abokin angon mai suna Ibrahim Idris, ya shaida wa Aminiya cewa angon Sulaiman Musa ya suma, amma bayan farfadowarsa sai aka sanar da shi cewa da Zainab za a yi auren a yanzu.

“An gabatar da ita a gare shi, nan take ya ce ya amince. Sai dai wani abin mamaki shi ne yadda tsohuwar budurwar ta saki jiki ta fadi bayan samun labarin daura auren da wata,” inji shi.

Kuma Amihad.com ta samu labarin ta yi yini biyu kwance a asibiti. Bikin ya yi armashi sosai fiye da yadda aka tsara yi da farko, sannan angon ya samu tarin kyaututtuka.

Amihad.com ta gano cewa angon da tsohuwar budurwar ’ya’yan wa da kanwa ne kuma a gidan su angon ta tashi. Sai dai daga baya an ce ta danganta lamarin da aljannu tare da yin nadamar abin da ta yi.

Leave a Comment