April 16, 2024

Safiya Chalawa, matar jarumin finafinan Kannywood, Adam A Zango ya bayyana ra’ayinta dangane da kasancewar mace matar aure a shafinta na Instagram.

A wallafar da tayi ranar Asabar, ta bayyana cewa abu ne mai matukar sanya mace murna ta kasance a cikin dakin mijinta kuma hakan yana kawo natsuwa mara misaltuwa.

Safiya Chalawa ita ce matar jarumin ta biyar wacce a yanzu haka ta haifa masa kyakkyawar yarinya mai suna Diana. An dade ana rade-radi yayin da wasu ke zargin cewa yadda su ka rabu da sauran matansa haka itama ba za ta dade ba, amma kuma sai ga shi sun ba mara da kunya.

Don yanzu haka zaune su ke lafiya kuma idan mutum yana bibiyar shafin jarumin da na matarsa, zai kula da yadda su ke yawan yabon juna. Tana yawan yabonsa tare da kiransa miji na gari mai halayen da ba ko wanne namiji ne yake da shi ba, kamar yadda ta fadi a ranar zagayowar haihuwarsa.

Shi ma yana yawan yabonta tare da cewa diyarsa za ta yi alfahari nan gaba idan ta ganta a matsayin mahaifiyarta. A wannan sabuwar wallafa da tayi, cewa tayi:

“Yar uwata musulma mai aure, a duniyar nan babu abinda yafi kasancewarki mamatar aure dadi. Ki kasance mai yawan yi wa Ubangiji godiya, da ya azurta ki da miji na kwarai, ki kuma dinga nuna farinciki akan kokarinsa (mijinki).

“Ki yi masa godiya akan taya ki cikasa addininki da yayi, bayan aurenki da yayi.”

Ta ci gaba da shawartar mata akan yadda za su tafiyar da rayuwar aurensu ta hanyar kyautata wa mazajensu. Muna fatan Ubangiji ya ci gaba da zaunar da su lafiya tare da fatan samun zuri’a dayyiba.

Hakika Allah ya wadata ka da abubuwan da maza da dama su ka rasa, Matar Adam Zango ga mijinta

Jarumi Adam A. Zango da matarsa Safiya Chalawa sun cika shekaru uku da aure a ranar Alhamis, 26 ga watan Mayun 2022 kamar yadda ta sanya a shafinta na Instagram.

Sun dinga yin wallafe-wallafe a shafukansu na sada zumunta su na nuna soyayya da matukar shaukin juna da su ke yi, wanda hakan ya dauki hankalin mutane da dama.

Sun dauki kyawawan hotuna sanye da kaya na gani da fadi tare da diyarsu, Diyana wanda hakan ya sa mutane su ka dinga yi musu sambarka.

LabarunHausa.com ta leka shafin matar Jarumin, Safiyya Chalawa na Instagram inda ta ga wani rubuto mai ratsa zuciya ta da yi wa mijinta akan kaunar da ta ke masa.

Ta fara da bayyana cewa mijin nata yana da abubuwa da dama da maza su ke nema amma sun rasa.

Ta ce tana matukar sonsa kuma da za ta iya rubuta littafi, za ta yi ne akan kyawawan halaye da fuskarka.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *