May 18, 2024

Balaraba Ganduje tayi min awon gaba da wasu muhimman takardun kadarori da ababen hawa – Miji

Mijin ‘yar gidan gwamnan Kano, Asiya Balaraba Ganduje, wato Inuwa Uba, yace Balaraba ta bude masa gida tayi awon gaba da wasu muhimman takardun kadarorinsa da suke Abuja da Kano, tare da wasu manyan motoci guda uku da mabudai, saboda haka yana bukatar a dawo masa da kadarorinsa kafin ya amince da sakin ta.

Inuwa ya bayyana haka ne ta bakin lauyansa a gaban kotun shari’ar musulunci dake filin Hockey a Kano, karkashin jagorancin mai Shari’a Khadi Abdullahi Halliru, a cigaba da zaman shari’ar da akeyi tsakaninsa da matarsa, wacce ta bukaci kotun ta raba aurensu, bayan shekaru goma sha shida a matsayin ma’aurata, kamar yadda jaridar Daily Nigerian rawaito.

To sai dai bangaren Balaraba, ta bakin lauyanta, Barista Ibrahim Nasarawa, ya musanta zargin awon gaba da kadarorinsa Inuwa, bayan amincewar biyan N50,000 a matsayin sadakin mijin, amma lauyan Inuwa yace basu yarda ba, a basu lokaci domin bayyana adadin kudin da za’a biya su.

Alkali ya bawa lauyan Inuwa mintuna 30 domin ya bayyana adadin kudin da suke bukata, wanda har lokacin ya cika bai samu damar bayyanawa ba, saboda haka aka dage zaman shari’ar har zuwa ranar 19 ga watan da muke ciki na Janairu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *