May 20, 2024

Wata mata da tayi Aure shekara 9 ba haihuwa ta haifi ‘ya’ya 5 lokaci guda.

Wata mata da ta kwashe tsawon shekaru 9 da aure ba tare da ta haihu ba, cikin Ikon Allah wannan karon ta haifi ‘ya’ya 5.

Matar mai shekaru 28 mai suna Chidinma AMAECHI ta haifi yara biyar ɗin ne maza 3 mata 2

Ta kuma haihu ne a ranar Alhamis da ta wuce a asibitin Life International Hospital dake Awka a jihar Anambra.
.Sai dai sai da aka yi mata aiki aka ciro ya’yan biyar.

Amma dukkansu suna cikin koshin lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *