June 15, 2024

Bidiyon Yadda Hadiza gabon ta kure Rara Da Tambayoyin
Fitacciyar jarumar Kannywood “yar asalin kasar Dubai, Hadiza Aliyu wadda akafi sani da Hadiza Gabon ta gayyaci fitacce kuma mashahurin Mawaƙin siyasar nan na Najeriya dama wajenta Dauda Kahutu Rarara wani shirin ta da take gabatarwa mai suna Gabon’s Room Talk Show.

Hadiza Gabon da Dauda Kahutu Rarara
Jarumar tayiwa Rarara din wasu zafafan tambayoyi wadanda ba’a taba yiwa Mawakin ba,duba da yanayin ka’idar Jarida,amma kuwa ita tayi har ta wuce Gona da iri.

Jarumar tayi masa tambayoyi kamar haka;

Wane ne Hankaka?
Wane karamin Sauro?
Shin Ganduje zai rushe gidanka?
Me yake faruwa tsakaninka da Abdul Amart?
Shin da gaske kai Kolo ne?
Ance kai Butulu ne wai?
Mene Gaskiyar magana akan kuna Soyayya da Aisha Humaira?
Haka da dai sauran tambayoyi da dama Hadiza Gabon din tayiwa Rarara din,zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa,kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *