June 15, 2024

Wata budurwa mai suna Bishira, ta rasa rayuwanta ana tsaka da kidan dj a wajen wani biki.

Budurwan ‘yar asalin jahan kano a unguwan jan bulo,ta rasa rayuwanta ne a lokacin da take suyan awara, a wajen sana’anta kwatsam saitaji kidan dj a wani gurin biki nan tayi tattaki zuwa wajen domin gane ma idonta.

Wanda abun ya faru a idonsu sukace da zuwanta gurin tafara liki da kudin cinikinta na awara, inda itama tafada fili tafara taka rawa bayan dj ya saka kida.

Shaidun gani da ido sukace, bishira ta fadi kasa wanwar ne a lokacin da take tsaka da tikan rawa kafin kace me rai yayi halin shi.

Lamarin ya matuƙar girgiza al’umma wannan wuri, inda aka tashi wannan taron sharholiyar na DJ babu shiri.

Rahoto Hajiya Mariya Azare

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *