June 19, 2024

CIKAN BURINA’ NASAMUN MURADINA WADDA YACIKA SIFFOFIN NAMIJIN DA NAKE SO YAZAMA MIJINA NA AURE.

Jama’a da dama musamman masu sha’awar kallon fina finan Hausa na masana’antar Kannywood na bayyana mabambantan ra’ayoyinsu akan jaruman masana’antar musamman mata.

Inda wasu ke cewa aure ne yafi dacewa dasu fiye da suzo suna yin shirin film yayin da a nasu ɓangare jaruman ke bayyana cewa Allah bai kawo lokacin auren ba don shi aure lokaci ne.

Apa Hausa Ta ruwaito cewa jarumar wato maryam yahaya ta bayyana hakanne lokacin da ake zancen daya shafi aure a Tsakanin Jarumai,

A nan shahararriyar jarumar masana’antar Maryam Yahaya tace ita fa sai ta samu namiji mai riƙo da addinin musulunci da ilimi, tsafta da tsoron Allah wanda zai riƙeta bisa gaskiya da amana sannan za tayi aure.

A wani labarin kuma.

A yunƙuri uku, majalisar wakilan Amurka ta kasa zaɓen shugaba

Majalisar Wakilan Amurka ta ɗage zamanta cikin yamutsi bayan yunƙurin da ta yi har uku na zaɓen Kevin McCarthy na jam’iyyar Republican a matsayin shugaba, ya ci-tura.

Wannan shi ne karon farko a ƙarni ɗaya da aka kasa zaɓen a ƙuri’ar farko.

Dan majalisa McCarthy, daga California, ya kasa samun rinjayen yawan kuri’un da ake bukata, 218, bayan da ‘yan majalisa 28 na jam’iyyarsa ta Republican suka juya masa baya, inda suka gwammace su zaɓi Jim Jordan a maimakonsa.

Sai dai duk da haka Mista McCarthy ya ce zai ci gaba da takarar har sai ya yi nasara.

A baya shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar, saboda haka ake sa ran ya zama kakakin a yanzu bayan da ‘yan Republican ɗin suka karɓe rinjaye da majalisar a zaɓen rabin wa’adi na watan Nuwamba.

Amma kuma idan aka ci gaba da rigima a takarar, to hakan zai tilasta wa ‘yan majalisar su nemi wani ɗan takarar daban.

Tasirin wannan koma bayan shi ne babu wani aiki da majalisar za ta iya gabatarwa har sai ta naɗa kakakinta.

A majalisar dattawan ƙasar kuma, ‘yan jam’iyyar Democrat mai mulkin ƙasar ke da rinjaye, abin da ke nufin ba lalle ne mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta ci gaba da kaɗa kuri’arta ba a duk lokacin da wani batu da ke gaban majalisar ya gamu da cikas.

Saboda a yanzu ‘yan Democrat ɗin na da ƙarin ƙuri’a guda da suka samu a zaɓen watan Nuwamba da aka yi a faɗin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *