April 16, 2024

China ta Yanke dangantaka da Amurka

China ta bayyana yanke wasu huldodin dangantaka da Amurka a fannoni da dama cikin su har da sauyin yanayi da yaki da safarar miyagun kwayoyi da harkokin soji.

Saboda ziyarar da shugabar Majalisar Dokokin kasar Nancy Pelosi ta kai Taiwan.

Kasar China ta dauki wadannan matakai ne cikin fushi saboda abin da ta kira katsalandar kan harkokin Taiwan sakamakon ziyarar bayan ta hakikance cewar, yankin mallakar kasarta ce.

Tun a ranar Alhamis daya gaba ta, tayi wa Taiwan kawanya da kayayyakin soji wajen kaddamar da atisayen soji,

matakin da ya gamu da suka daga Amurka da kawayenta na sassan duniya.

Labarai Masu Alaka: Matsalar Tsaro: Osinbajo Ya Bukaci Sojoji Da Suyi Bayanin Kudaden Da Suka Basu

A wannan Juma’ar, Kasar China ta hannun Ma’aikatar Harkokin Wajenta, ta cacaki Amurka wajen dakatar da tattaunawa da hadin kai tsakanin kasashen biyu, ciki kuma har da batun da ya shafi sauyin yanayi.

China ta bayyana yanke wasu huldodin dangantaka da Amurka
China ta bayyana yanke wasu huldodin dangantaka da Amurka

Ta kuma kara sanya takunkumi akan Nancy Pelosi saboda ziyarar, yayin da ita kuma take kare matakin da ta dauka na zuwa Taiwan, inda take cewa matsayin Amurka bai sauya akan kasar ba.

Yayin mayar da martani, Taiwan ta bayyana takaicinta da matakin da China ta dauka cikin fushi,

inda Firaministan yankin Su Tseng- chan ya roki abokan huldarsu da su kawo karshen tankiyar da ake samu a tsakanin su.

Karanta Wannan: Sunusi Lamido – Najeriya Ta Tabar-bare Fiye Da Yadda Take A 2015

Ku Cigaba Da Bibiyar Wannan Shafi Domin Samun Sahihan Labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *