June 19, 2024

Labarin ban Al’ajabi tsakanin wani saurayi mai kimanin shekaru talatin da biyar dan kasar china da wata budurwa yar asalin jihar kano mai kimanin shekaru 25 a duniya.

Matashin dai ya kasance dan asalin kasar China ne dake zaman shi, a kasar nigeria cikin jihar kano domin gudanar da ayyukan shi tsakanin shi da wasu kamfanoni a jihar.

Saurayin ya kasance mutum mai matukar kishin akan budurwar da yake da burin aurenta saidai ashe bayan shi akwai wani mutum daya kasance tana soyayya dashi dan asalin jihar kaduna dake nigeria.

Haka zalika har takai ga anfara shirye shiryen auren ta amma bata sanar dashi ba saboda tana tsoron abinda zai biyo baya sakamakon kishin da yake nunawa agareta.

Amma ajiya ne sai yayi karo da status din babbar kawar budurwar tashi a shafin sada zumunta na WhatsApp, yayin da yake ganin an wallafa photunan ta tare da mutumin da zata aura kwanan nan.

Hakan yayi matukar fusata shi yayin daya garzaya izuwa unguwar su, da misalin karfe 12:00 na daren juma’a domin hallakar da rayuwar ta domin kowa ya rasa ta cewar saurayin dan kasar China.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *