May 24, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/hurvr/public_html/wp-content/themes/chromenews/lib/breadcrumb-trail/inc/breadcrumbs.php on line 253

DA ƊUMI-ƊUMI: Wasù ManyanńMalamai Na Ganawar Sirri Dòmin Ba Da Umarni A Zaɓi Gawuna

Rahotannin da ke zuwa mana yanzu haka na bayyana cewa wasu jiga-jigan malamai su na tattaunawar sirri da junansu yanzu haka a Jihar Kanò domin duba yiyuwar ba da umarnin a zaɓi ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a Zaben ranar Asabar.

Majiya mai tushe da ta nemi mu sakaya suna, ta tabbatar mana da cewa zuwa yanzu Malaman sun cimma matsaya cewa Jahar Kanò a halin yanzu ta na buƙatar shugaba ne mutum kamili mai dattako, jajirtacce, mai haƙuri, mai gaskiya mai juriya da himma wanda zai rungumi kowa da kowa ya yi tafiya tare da su batare da nuna bambanci da wariya ba.

Majiyar ta cigaba da cewa zuwa nan gaba kaɗan ake sa ran malaman za su ƙarƙare zaman tare da fidda matsaya guda wadda za su ba wa al’ummar jihar kanò da mabiyan su shawarar zabar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

Sauran bayanan na nan tafe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *