June 9, 2024

A kullum wannan soyayyar kara ƙarfi take tsakanin wannan jaruman biyu saboda duk inda suke zaka gansu tare sun zama tamkar miji da mata basa rabuwa wanda mawaka suke cewa hanata da jini tilas sai an barmu wannan dai soyayyar tayi karfi sosai.
Yayinda ake ta bukukuwa a wannan masana’anta suma ana saran Nanda wani lokaci kadan za’a iya ganin katin gayyara nasu domin ana zargin akwai abinda suke kullawa ta karkashin kasa domin alakar kullum kara kauri take kowa yanason kowa.

An kasa gane gaskiyar abin inda suke cewa ƙawance ne wasu kuma suke cewa soyayya ce to koma dai mene Nanda wani lokaci zamusan komai kuma da zarar mun sani zamu sanar da masu biye damu.


Wanna alakar tasu tafi ƙarfin ka kirata da ƙawance domin hatta hutun shekarar nan tare sukayi a kasar Dubai sannan kuma tayi shagalin bikin birthday wanda shine wanda ya habaka mata cake wannan abu sai girma yake.

Mudai koma meye abinda zamu iya cewa shine Allah ya tabbatar da alkhairi saboda wamnan alaka tafi ƙarfin wasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *