April 15, 2024

Da Dumi-Dumi Tinubu Ya Zabi Kashim Shettima A Matsayin Mataimaki

“Labarin da muke samu da dumi-dumin sa ya tabbatar da cewa dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC,

Bola Ahmed Tinubu ya zabi Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa”.

“Bola Tinubu ya sanar da hakan ne bayan ya gana da Shugaban Kasa Buhari a Daura a yau Lahadi”.

Za mu kawo muku karin bayani nan bada jimawa ba.

Kungiyar ASUU zata janye yajin aiki

2023: Tinubu Ya Amince Zai Dauki Musulmi A Matsayin Mataimakinsa

Tinubu
JAGABA

Rahotanni sun bayyana cewar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Ya amince da daukar Musulmi a matsayin wanda zai masa takarar mataimaki a zaben shekarar 2023.

Wata majiya mai karfi a Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu, wacce ta bukaci a sakaya sunanta,

ta tabbatar wa da Kamfanin Dillacin Labarai (NAN) hakan a yau Lahadi a Abuja.

Majiyar ta shaida wa NAN cewa “Tinubuzai bayyana sunan mataimakin takararsaa makon da za a shiga”.

A baya bayan nan, anyi ta muhawara a kasa kan addinin “yan takarar shugaban kasa da abokan takararsu”.

Sai dai kuma Tinubu ya dauki Kabiru Ibrahim Masari daga jihar Katsina a matsayin wanda zai masa mataimaki na wucin gadi.

Yin takarar Musulmi biyu a matsayin shugaba da mataimaki ya tada kura, musamman a yankin kudancin Nijeriya,

wanda suke ganin hakan kamar rashin adalci ne ga nasu yankin da kuma addinin.

Da Dumi-Dumi An Kashe Mutane 15 A Mashayar Giya Afrika ta Kudu

Afirka
Afirka Ta Kudu Ankashe Mutane 15

Akalla mutane 15 ne aka bindige har lahira a unguwar Orlando ta Gabas da ke garin Soweto a Afirka ta Kudu.

“Wani rahoto ya nuna cewar wasu mutane da dama na cikin mawuyacin hali a asibiti bayan harin”.

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun shiga mashayar ne da sanyin safiyar yau Lahadi,

inda suka fara harbe harbe a kan wasu matasa kafin daga bisani suka gudu a cikin wata farar karamar mota bas.

Rundunar yan sandan yankin tace har yanzu ba ta gano dalilin kai harin ba.

Elias Mawela, shugaban yan sanda na lardin Gauteng,

ya bayyana lamarin a matsayin harin abun takaici a kan ma’aikatan da ba su ji ba su gani ba.

Ya kara da cewa maharan na dauke da bindigu da harsashi kirar 9mm a lokacin da suka shiga mashayar.

Bincike na farko ya nuna cewa mutanen suna jin dadin kansu a cikin gidan ruwa, in ji shugaban yan sanda.

Sai kawai suka shigo suka harbe su, Kwatsam, sai suka ji karar harbe harbe, a lokacin ne mutane suka yi kokarin fita daga mashayar.

Bamu da cikakkun bayanai a halin yanzu na dalilin da ya sa suka kashe wadannan mutane.

Za kaga an yi amfani da babbar bindiga ba kakkautawa,

kuna iya ganin cewa kowane dayan wadannan mutanen yana cikin firgici.

Yawan harsashin da aka samu a wurin ya nuna gungun mutane ne suka harbe mutanen.

A wani harin da aka kai a wata mashaya dake lardin KwaZulu Natal da ke kudu maso gabashin kasar,

an kashe wasu mutane hudu.

Har yanzu dai yan sandan ba su damke wa’inda suka kai harin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *