Da Dumi Dumi Yanzu Yanzu Manyan Malaman Jahar Kano Sun Bada Umarnin Dole Ne A Zaɓi Dr Nasiru Yusuf gawuna..

Da Dumi Dumi Yanzu Yanzu Manyan Malaman Jahar Kano Sun Bada Umarnin Dole Ne A Zaɓi Dr Nasiru Yusuf gawuna

DA ƊUMI-ƊUMI: Wasù ManyanńMalamai Na Ganawar Sirri Dòmin Ba Da Umarni A Zaɓi Gawuna

Rahotannin da ke zuwa mana yanzu haka na bayyana cewa wasu jiga-jigan malamai su na tattaunawar sirri da junansu yanzu haka a Jihar Kanò domin duba yiyuwar ba da umarnin a zaɓi ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a Zaben ranar Asabar.

Majiya mai tushe da ta nemi mu sakaya suna, ta tabbatar mana da cewa zuwa yanzu Malaman sun cimma matsaya cewa Jahar Kanò a halin yanzu ta na buƙatar shugaba ne mutum kamili mai dattako, jajirtacce, mai haƙuri, mai gaskiya mai juriya da himma wanda zai rungumi kowa da kowa ya yi tafiya tare da su batare da nuna bambanci da wariya ba.

Majiyar ta cigaba da cewa zuwa nan gaba kaɗan ake sa ran malaman za su ƙarƙare zaman tare da fidda matsaya guda wadda za su ba wa al’ummar jihar kanò da mabiyan su shawarar zabar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

Sauran bayanan na nan tafe.

KAR MU YIWA KAURAN BAUCHI BUTULCI

‘Yan Bauchi ku fadi gaskiya tsakaninku da Allah tun da aka dawo tsarin Mulkin Demokaradiyyah bayan tsohon Gwamnan Bauchi Ahmad Adamu Mu’azu ya gushe mun sake samun Gwamnan da yayi aiki a zahiri kamar Sanata Bala Muhammad Abdulkadir Kauran Bauchi?

Ba za’a rasa wasu kura-kurai a Gwamnatin Kaura ba kamar yadda ake samu a cikin kowace irin Gwamnati, amma ana duba abinda yafi yawa ne, ba shakka aikin da Kaura yake yi a Bauchi ya wuce gaban misali

Ku bar batun tsohon Soja Sarkin Bindiga mijin Ministan jinkai, ba dan siyasa bane, bai san administration ba, har ya kare Gwamnatinsa da wahala ya tabuka komai, aikin soja ya sani

Magana ta gaskiya Kauran Bauchi ya zuba aikin da ya cancanci mu sake bashi dama a karo na biyu, a fahimtata bai kamata ‘yan Bauchi mu yiwa Kaura butulci ba

Ku zo mu sake zaben Kauran Bauchi da alheri domin ya zarce

Leave a Comment