Da Na Auri Talaka Gara Na Mutu Banyi Aure Ba – Cewar Fatima Sheka

Wata Matashiya yar arewacin na Najeriya mai suna Fatima Sheka ta ce da ta auri talaka Gara ta mutu ba tayi aure ba. Matashiyar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter.

To sai dai wannan rubutu da tayi ya dau hankali sosai a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama sukayi ta bayyana ra’ayinsu kan hakan.

Jarumar tayi wallafa kamar haka “Nifa Idan Har Talaka Zan Aura, To Gwara Na Mutu Ban Yi Auren Ba” a Cewar Fatima Sheka.

Sai dai babu wuya da fadin hakan da tayi masu amfani da dhafin Facebook suka sakata a gaba, wasu suna ganin ai hakan da ta fada ra’ayin ta ne ba nawani ba, a yayin da wasu kuma banda zagi da tsinuwa babu abunda sukeyi.Wannan ba shi ne karon farko da ake samun irin wannan wallafar a shafukan sada zumunta ba, musanman wajen yan matan Arewacin Najeriya.

Leave a Comment