May 18, 2024

Innalillahi Gaskiya Wannan Ba Tarbiyya hausawa Bace Kalli Yadda Amarya Take Rawar Iskanci Agaban Kowa

YADUWAR ZINA ACIKIN AL’UMMAH.

Wasu daga cikin dalilan da suka sa wannan bala’i ta zina ta yawaita cikin AL’UMMAH.

  1. TALLE: Mafiya yawan yara matan dake yawon talle a cikin kasuwanni, Garejoji, Tashoshin mota, da Unguwanni suna cikin hatsarin afkawa cikin wannan mummunar dabi’a. Ba don komai ba sai saboda yadda kullum zasu rika jin kalamai na batsa da kuma miyagun wasanni irin na batsa da suke samu daga shashashun samari da kuma tsofaffin yan tasha.

WAYOYIN SALULA: Wayoyin salula suna taka mummunar rawa cikin yaduwar fasadi da lalacewar tarbiyar AL’UMMAH. Musamman ta bangaren HOTUNA da VIDIYO NA BATSA da recording na kalmomin batsa wanda matasa maza da mata suke turawa a wayoyinsu. Yara Qanana sukan kalli hotunan yadda ake jima’i. Daga nan kuma sai shedanci ya shiga zukatansu su fara tunanin hanyoyin da zasu bi su rika samun biyan bukatarsu, alhali da can irin wannan tunanin bai taba shiga kwakwalwarsu ba.

YADUWAR FINAFINAI: Yaduwar Finafinaina waje da kuma na gida shima ya taimaka wajen watsewar al’amura. Ba don komai ba, idan ka lura da yadda rayuwar Matan hausawa take acikin shekarun 1980 zuwa 2000 zaka ga ba daidai take da wacce mukeyi yanzu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *