Dan Majalistar Tarayya ya baiwa matashiyar da tazo na 2 a gasar karatun Al-Qur’ani kyautar Mota

Dan Majalistar Tarayya ya baiwa matashiyar da tazo na 2 a gasar karatun Al-Qur’ani kyautar Mota

Dan Majalistar Tarayya ya baiwa matashiyar da tazo na 2 a gasar karatun Al-Qur’ani kyautar Mota  kirar 406

A ‘yan kwana kin nan abin farin ciki da murna yana yawan faruwa da ‘yan mata wanda suke haddace Al-Qur’ani mai girma, wasu daga cikin sukan rubuta sji da hannun su.

To a yau ma dai mun sami wani labarin akan wata matashiyar yarinya wanda tayi nasarar zuwa na biyu 2 a gasar karatun Al-Qur’ani mai girma da aka gudanar.

Wanda har Dan Majalistar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Lere “Injiniya Ahmad Munir” ya yiwa Dalibar kyautar Motar kirar 406.

A Wani Labarin Na Daban Kuma
Shekaruna Ashirin Da Ukku Ina Gadin Maƙabarta Albashina Naira Dubu Biyu Ne A Wata…Malam Ali

A wata tattaunawa da mukayi da Malam Ali da yake kula da Maƙabartun Ɗan Takum sabuwa da tsohuwa ya shaida mana cewa an ɗauke shi aiki ranar 11/11/1999 an fara biyan shi Naira Dubu Ɗaya a matsayin Albashi bayan zuwan Hon. Hamisu Gambo ne aka maida masu Naira Dubu Biyu tun daga nan har kawo yanzu abinda ake biyan su kenan babu ƙari.

Ali yace su kimanin Bakwai ne suke aikin kula da waɗannan Maƙabartun amma Albashin su Naira Dubu Biyu Ne kachal a wata, kuma su babu Mai kulawa dasu sunajin ana cewa ana kulawa da Maƙabartu amma su dai basu ga komai ba.

A yayin wannan ziyarar mun tarar da ayyukan Alkhairi da wasu bayin Allah sukeyi Ɗaya daga cikin su shine wani Bawan Allah da yazo ya sanyawa Maƙabartar Ɗan Takum Fitilu da suke haskaka ƙaburburan idan dare yayi, a halin yanzu kuma wani bawan Allah yana ƙoƙarin gina famfon burtsatse tare da azamata tankin ruwa, Allah ya saka masu da Alkhairi Amin.

Wannan bayanin na Malam Ali yasa na fatsama neman ƙarin haske akan Lamarin nan ga kuma Ƴan bayanan da na kalato;

Sarkin Gobirawa daya ne daga cikin Mutanen da suke kula da Maƙabartun faɗin ƙaramar hukumar Katsina yayi mani bayani dalla dalla yadda Al’amarin yake tafiya.

A ta bakin shi ya tabbar da cewa lallai Naira Dubu Ɗaya itace aka fara da ita a matsayin Albashi domin a cewar shi Nima gadon aikin nan nayi nasan sadda aka maida Naira Dubu Biyu, amma daga baya akwai wani ƙwamitin kula da Maƙabartun da aka kafa Wanda nima member ne a ciki.


Shi wannan ƙwamitin yana zagayawa ne wajen masu hannu da shuni domin neman Gudummuwar su akan su taimaka ma Maƙabartun, yace suna zagaya wurin Mutane daban-daban wasu sun ɗauki Alƙawalin cewa zasu riƙa ɗaukar nauyin Mutum Biyu wasu Ukku wasu Ɗaya gwalgwadon Iko, a cewar shi akwai wani bawan Allah da yanzu baya raya duk sadda ya fidda zakka yakan ware wani kaso yace a rabama masu kula da Maƙabartu, sannan kuma Alh. Dahiru Mangal duk watan Azumi yana bada kayan Abinci a rabama masu kula da Maƙabartun.

SHIN WAKE DA ALHAKKIN KULAWA DA MAƘABARTUN….

Na tuntubi ɓangaren Gwamnati wato ƙaramar hukumar Katsina domin jin ta bakin su, wani Jami’in Gwamnatin da muka tattauna dashi yace lallai ƙaramar hukuma itace take da alhakkin kulawa da Maƙabartun kuma akwai ƙwamitin da ta kafa domin tantance yawan Mutanen da suke kulawa da Maƙabartun kuma shi yana cikin ƙwamitin da sukayi aikin tantancewar, sai dai kamar yadda yace lallai kuɗaden da ake biyan masu gadin gaskiya baida yawa domin bai isa Mutum yace ya dogara dashi ba dole sai dai ya nemi wata sana’ae domin rufama kai Asiri.

A cikin bayanan shi ya tabbar mani da cewa akwai ƙwamitin kula da Maƙabartun da shi ake baiwa kuɗin shi kuma ya haɗa da abinda ya samu ya biya Albashin masu gadin.

Na sake tuntubar Sarkin Gobirawa akan hakan ya tabbar mani da cewa lallai haka Lamarin yake kuma a baya har ƙarin Albashi anyi zuwa Dubu Biyar daga baya kuma ya koma Dubu Huɗu da Ɗari Biyar zuwa Dubu Huɗu, daga baya kuma bayan kimanin Shekara Guda wannan tsari ya Sha Ruwa.

Ya ƙara da cewa a halin da ake ciki akwai masu gadin Maƙabartun da suke mashi koken kimanin watanni Ukku zuwa Huɗu ba’a basu Albashi ba, yayi mani ƙarin haske akan dalilin da yasa ba’a basu Albashin ba, Sarkin Gobirawa yace dalilin shine Alh. Bilya Sanda shine yayi Alƙawalin cewa zai ɗauki Mutane Hamsin domin su riƙa kula da gadin Maƙabartun kuma zai biya su Albashin wata shidda sai dai har kayo yanzu bamu ƙara jin wani bayani daga wurin shi ba, Lamarin da yasa hatta da sauran kuɗaden da ake samu daga sauran wurare yanzu haka suna nan aje bamu biya waɗanda ke akwai ba balle mu ɗauki wasu ƙarin masu gadin.

Wannan lamari yasa jikina yayi sanyi, sai dai wasu sunce ai dama da yawa sunayin aiki ne kamar na sakai domin neman Lada, sannan kuma idan Waɗanda akayi ma rashi sunzo domin ginar ƙabari toh akanyi ciniki da wanda zai haƙa a biyashi wannan shine hanyar da suke Ɗan samun wani abu sai kuma masu saida tukwane Suma a saya a biya su.

Kira na Musamman ga Al’umma dan Allah wanda yake da halin da zai iya taimakawa Mutanen nan toh idan dama ta samu ya taimaka masu lokaci zuwa lokaci Wanda Allah ya ci da.

Leave a Comment