Gwanin ban sha’awa yadda wasu matan Kannywood ke tarairayar mazajen su

Aure yayi albarka wasu jarumai mata da sukai shuhura a Kannywood sun nuna yadda suke jin dadin Aure su da kuma nuna soayyar su ga mazajen su.

Wani abun ban mamaki da mutane ke gani a game da jaruman yadda suka iya zaman Aure suka hakura da harkar fim duk da cewar an chanfa yan fim basa iya zaman aure.

Wannan jarumai dai sun hada da Maryam Ab Yola da Maryam Wazeery, Duk wanda yasan wannan jaruman yasan taurarun su suna tsaka da haskawa Allah ya kawo musu mazajen Aure

Jaruman biyu sunyi wata wallafa a shafukan su inda daya ta wallafa hoton ta tare da mijin ta gami da karuwar da suka zasmi na da namiji.

Ita kuwa Maryam Ab Yola ta wallafa hoton da wani gajeran Bidiyon wanda sukai tare da mijin nata.

Leave a Comment